Fusatattun Matasa Sun Cafke Yan Fashi Sun Cinna Musu Wuta Har Lahira a Jihar Kano

Fusatattun Matasa Sun Cafke Yan Fashi Sun Cinna Musu Wuta Har Lahira a Jihar Kano

Kano:- Wasu fusatattun matasa a jihar Kano sun sheke wasu da ake zargin yan fashi da makami ne, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Matasan sun cinnawa yan fashin wuta da ransu a ƙauyen Rimi, karamar hukumar Sumaila, jihar Kano.

Rahotannu sun bayyana cewa wasu yan fashi su uku sun kai hari ƙauyen Rimi amma matasan suka tare su, yayin da suka kame biyu ɗaya ya tsere.

Fusatattun Matasa a Kano sun kona yan fashi
Fusatattun Matasa Sun Cafke Yan Fashi Sun Cinna Musu Wuta Har Lahira a Jihar Kano Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Matasan dake a fusace sun cinnawa waɗanda suka kama wuta bayan sun lakaɗa musu mugun duka.

Meyasa matasan suka ɗauki doka a hannunsu?

Kakakin hukumar yan sanda na jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

A cewar DSP Kiyawa, hukumar yan sanda ta samu rahoton cewa wasu gungun matasa sun cinnawa yan fashi guda biyu wuta.

Me yan sanda suka yi?

Kakakin yan sanda ya bayyana cewa jami'ai sun isa wurin a makare, sun tarad da yan fashin sun kone kurmus amma sun ɗauki ragowarsu zuwa Asibiti.

Kara karanta wannan

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Masu Garkuwa, Sun Kame Wasu a Benuwai

DSP Kiyawa yace:

"Mun sami wukake da wasu makamai a wurin da lamarin ya faru wanda mallakin yan fashin ne."
"Zuwa yanzun kwamishinan yan sandan Kano, Samaila Shuaibu Dikko, ya bada umarnin gudanar da bincike."

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: