'Yan Bindiga Sun Hallaka Jam'in Tsaro, Sun Cinnawa Ofishin 'Yan Sanda Wuta

'Yan Bindiga Sun Hallaka Jam'in Tsaro, Sun Cinnawa Ofishin 'Yan Sanda Wuta

  • Ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hare-hare a jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
  • Miyagun ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a ƙaramar hukumar Obowo ta jihar sun hallaka wani jami'in ɗan sanda
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar harin ya ce a bi sahun ƴan bindigan domin cafke su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Wasu ƴan bindiga a daren Talata sun kashe wani jami'in ɗan sanda a jihar Imo

Lamarin ya faru ne a kwanar NEPA dake Umulogho a ƙaramar hukumar Obowo a jihar.

'Yan bindiga sun kai hari a Imo
'Yan bindiga sun hallaka dan sanda a jihar Imo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa sai da ƴan bindiga suka fito da ɗan sandan daga ɗakinsa kafin su kashe shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari sakatariyar karamar hukuma, sun hallaka jami'an tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta ce ƴan bindigan sun tabbatar da cewa ba a samu wani ɗan sanda da ke zaune a gidan ba.

"Sun tafi ne bayan sun shafe kusan mintuna 45 suna cin karensu babu babbaka ba tare da wata tangarɗa ba, sun riƙa yin harbi lokaci bayan lokaci domin tsorata mutane."

- Wata majiya

Jaridar The Nation ta ce bayan kashe ɗan sandan, ƴan bindigan sun dawo da safe inda suka ƙona ofishin ƴan sanda na Otoko da ke kan hanyar Owerri zuwa Umuahia.

An samu hare-hare da dama da ƴan bindigan suka kai a jihar Imo a ranar Talata, inda suka kashe jami’an tsaro biyu a sakatariyar ƙaramar hukumar Isiala Mbano, tare da ƙona motoci a harabar sakatariyar.

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Imo, ASP Henry Okoye, ya ce za a kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su gaban kotu.

Kara karanta wannan

Kifar da Tinubu: Ƴan sanda sun mayar da martani kan ikirarin Baturen da ake nema

Ya ce an tura tawagar ƙwararrun jami'ai zuwa yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin mazauna yankin.

Ƴan bindiga sun kai hari a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kashe mutane shida a Congo, wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Plateau.

A cewar mazauna yankin, lamarin ya faru ne a kasuwar garin da misalin karfe 7:00 na yamma, inda ƴan bindigan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng