Farashin Fetur: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar da Martani ga Kungiyar Kwadago NLC

Farashin Fetur: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar da Martani ga Kungiyar Kwadago NLC

  • Fadar shugaban ƙasa ta musanta ikirarin ƴan kwadago cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya karya alƙawarin da ya ɗauka kan farashin mai
  • Kungiyar kwadago, NLC ta bayyana cewa Tinubu ya yi masu alkawarin ba za a ƙara farashin fetur ba kafin amincewa da albashin N70,000
  • Hadimin shugaban ƙasa, Abdul'aziz Abdul'aziz ya ce ya halarci duka tarukan da Tinubu ya yi da NLC kuma babu inda aka yi maganar fetur

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Fadar shugaban kasa ta musanta zargin da kungiyar kwadago NLC ta yi cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karya alkawarin da ya ɗauka kan fetur.

A wata sanarwa da NLC ta fitar ranar Talata, ƙungiyar kwadagon ta yi iƙirarin cewa Shugaba Tinubu ya saɓa alƙawarin da ya ɗauka na daidaita farashin fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

An bukaci Tinubu ya kori manyan ministoci 2 a gwamnatinsa, an fadi sunayensu

Yan kwadago da Tinubu.
Hadimin shugaban kasa ya musanta zargin Tinubu ya ci amanar ƴan Najeriya game da farashin fetur Hoto: Nigeria Labour Congress HQ, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mai taimakawa shugaban kasar kan harkokin watsa labarai, Abdul'aziz Abdul'aziz ya musanta wannan iƙirari na NLC a shafinsa na manhajar X ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan farashin litar man fetur ya tashi a gidajen man NNPC daga N568 zuwa N855.

Fadar shugaban ƙasa ta karyata NLC

Hadimin shugaban ƙasar ya yi watsi da ikirarin NLC, inda ya bayyana shi a a matsayin, "siyasa mara tsafta," saboda babu inda Tinubu ya ɗauki wannan alƙawarin.

Abdul'aziz ya ce ya halarci taruka da ƴan kwadagon suka yi da shugaban kasa kuma ko kaɗan ba a taɓo batun farashin man fetur ba.

Ya ce:

"Na shiga taruka biyu da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi da ƴan kwadago, babu wani tayi ko yarjejeniya da aka yi game da farashin man fetur.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga tsaka mai wuya, jam'iyya ta fara shirin ɗaukar mataki a kansa

"Kwamared Ajaero ya sake dawowa da kazamar siyasarsa, zai yi wasa da tunanin ƴan Najeriya."

Wane alƙawari Shugaba Tinubu ya karya?

NLC dai ta zargi shugaba Tinubu da cin amanar ‘yan Najeriya ta hanyar kara farashin man fetur duk da alkawarin da ya yi na tabbatar da daidaiton farashi.

A cewar kungiyar kwadago, muhimmin sharaɗin da suka shinfiɗa wajen karbar mafi karancin albashin N70,000 shi ne tabbacin farashin man fetur ba zai tashi ba.

Sai dai Abdulaziz ya musanta wannan ikirari na NLC, yana mai jaddada cewa babu wani alkawari da shugaban kasar ya yi game da farashin fetur.

MAN ta koka kan tsadar fetur

A wani labarin ƙungiyar MAN ta bayyana cewa farashin abinci da sauran kayayyakin amfani zai ƙara tashi saboda tsadar litar man fetur.

Kamfanin mai na ƙasa (NNPC) ya ƙara farashin litar fetur daga N568 zuwa sama da N800 duk da ba a sanar da sauyin farashin a hukumance ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262