MAN Ta Koka kan Tsadar Fetur, Ta Jero Kayayyakin da Za Su Ƙara Tashi a Najeriya

MAN Ta Koka kan Tsadar Fetur, Ta Jero Kayayyakin da Za Su Ƙara Tashi a Najeriya

  • Kungiyar MAN ta bayyana cewa farashin abinci da sauran kayayyakin amfani zai ƙara tashi saboda tsadar litar man fetur
  • Kamfanin mai na ƙasa (NNPC) ya ƙara farashin litar fetur daga N568 zuwa sama da N800 duk da ba a sanar a hukumance ba
  • Wannan ƙari dai ya tayar da hazo a sassan kasar nan, inda kungiyar kwadago ta buƙaci gwamnati ta gaggauta canza tunani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kungiyar masu masana'antu a Najeriya (MAN) ta bayyana cewa da yiwuwar farashin kayayyaki su ƙara hauhawa sakamakon ƙarin farashin man fetur.

Wannan na zuwa ne bayan tashin farashin litar man fetur daga N568 zuwa kusan N855 a gidajen mai mallakin kamfanin NNPC.

Kara karanta wannan

Farashin Fetur: Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani ga kungiyar ƙwadago NLC

Farashin abinci.
MAN ta ce tsadar mai ka iya ɗaga farashin kayayyaki a Najeriya Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, tsadar man feturin tashi guda ya jawo surutu a faɗin Najeriya, inda kungiyar kwadago NLC ta buƙaci a soke ƙarin nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MAN ta faɗi kayayyakin da za su tashi

A wata sanarwa da shugaban MAN, Segun Ajayi-Kadir, ya fitar ranar Laraba, ya yi bayanin yadda tashin farashin man fetur zai shafi al'umma a Najeriya.

"Dangane da tasirin da ka iya biyo bayan tsadar fetur, idan muka duba abin da ya saba faruwa kuɗin sufuri zai tashi, haka farashin kayayyaki da na abinci za su kara hauhawa.
"A duk lokacin da mai ya kara tsada, kuɗin sufuri da wutar lantarki zasu ƙaru, wanda hakan zai rage kuɗin shiga a hannun mutane.
"Har ila yau raguwar kuɗin shiga a hannun jama'a zai rage yawan buƙatu da sayen kayayyaki kuma hakan babbar illa ce ga ƴan kasuwa a kowane ɓangare."

Kara karanta wannan

Awanni da sanarwar NNPC: Zanga zanga ta barke a Kano yayin da fetur ta kai N1200

Shugaban MAN ya kuma nuna danuwa kan illar da hakan za ta haifar a ɓangaren masana'antu waɗanda dama tuni ayyukansu suka ja baya, rahoton The Nation.

Litar fetur ta haura N1,000 a Kano

A wani rahoton kuma ƙarancin man fetur ya ƙara tsananta yayin da farashin lita ya kai N1,200 a gidajen man ƴan kasuwa a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa farashin ya tashi zuwa N904 a gidajen man kamfanin NNPCL, masu ababen hawa sun yi layi suna jira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262