'Yan Bindiga Sun Kai Hari Sakatariyar Karamar Hukuma, Sun Hallaka Jami'an Tsaro
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki a sakatariyar ƙaramar hukumar Mbano-Isiala da ke jihar Imo
- Ƴan bindigan sun hallaka jami'an tsaro biyu tare da ƙona sassan sakatariyar da wasu motocin da aka ajiye a harabar ta
- Wata majiya ta ce harin bai rasa nasaba da zaɓen tsaida gwani na PC domin zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Imo - Wasu ƴan bindiga sun kashe jami’an tsaro biyu a sakatariyar ƙaramar hukumar Isiala-Mbano da ke jihar Imo.
Ƴan bindigan sun mamaye yankin ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Talata inda suka yi ta harbe-harbe.
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
Jaridar The Cable ta rahoto cewa wata majiya ta ce maharan sun kashe jami’an tsaro biyu da ke bakin aiki tare da ƙona wasu sassan ginin sakatariyar da motoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da cewa, mai yiwuwa harin ya faru ne sakamakon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a ƙananan hukumomi 27 da mazaɓu 306 na jihar.
"An harbe jami'an tsaro biyu a sakatariyar ƙaramar hukumar Isiala-Mbano har lahira. Ƴan bindigan sun kuma ƙona wani yanki mai girma na sakatariyar da wasu motoci da aka ajiye a harabar."
"Jam’iyyar APC na gudanar da zaɓen fitar da gwani na ƙananan hukumomi domin zaɓen ranar 21 ga watan Satumba. Wataƙila maharan sun yi tunanin ana gudanar da zaɓen ne a sakatariyar."
"Sun kai farmaki wurin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare inda suka harbe jami’an tsaron da suka gani har lahira. Wasu da dama kuma sun tsere da raunuka daban-daban."
- Wata majiya
'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro?
Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Imo, Henry Okoye, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya tabbatar da aukuwar harin inda ya bayyana cewa ba a kashe jami'an tsaro ko ɗaya ba, amma an raunata ƴan banga mutum biyu.
"Jami'an ƴan sanda tare da ƴan banga sun samu nasarar fatattakar ƴan bindigan, sai dai abin takaici sun jefa wani abin fashewa wanda ya ƙona wani sashe na ginin sakatariyar tare da motocin da aka ajiye a wajen."
- Henry Okoye
Ƴan bindiga sun hallaka shugaban jam'iyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka wani shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Ƴan bindigan sun hallaka Mista Sunday Oche wanda shi ne shugaban jam'iyyar Labour Party a Igumale cikin ƙaramar hukumar Ado ta Benue.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng