Kifar da Tinubu: Ƴan Sanda Sun Mayar da Martani kan Ikirarin Baturen da Ake Nema

Kifar da Tinubu: Ƴan Sanda Sun Mayar da Martani kan Ikirarin Baturen da Ake Nema

  • Rundunar ƴan sanda ta musanta ikirarin baturen nan ɗan kasar Burtaniya da ake zargi da ƙulla makircin kifar da gwamnatin Bola Tinibu
  • Mai magana da yawun ƴan sanda, Olumuyiwa Adejobi ya ce sun gayyaci baturen sau da dama tun kafin ayyana nemansa ruwa a jallo
  • Ƴan sanda na neman Andrew Wynne ruwa a jallo kan zargin cin amanar ƙasa da ɗaukar nauyin ta'addanci, lamarin da ya musanta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bukaci dan kasar Burtaniya da ake nema ruwa a jallo, Andrew Wynne, da ya fito daga inda yake boye ya mika kansa. 

‘Yan sanda sun kuma musanta ikirarin Wynne cewa ba a gayyace shi ba kafin a ayyana shi a matsayin wanda ake nema.

Kara karanta wannan

"Ka bi a hankali": Gwamnan PDP ya gargadi kwamishinan 'yan sanda

Wynne da kakakin ƴan sandan Najeriya.
Rundunar ƴan sanda ta bukaci baturen da ake nema ruwa a jallo ya miƙa kansa cikin ruwan sanyi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Idan ba ku manta ba rundunar ƴan sanda ta ayyana neman Wynne da abokin harkallarsa ɗan Najeriya Lucky Obiyan bisa zargin kitsa tuggun kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar Yan sanda ta sa ladan N20m

Daily Trust ta kawo cewa rundunar ƴan sanda ta sanya ladan N20m ga duk wanda ya ba da bayanan wurin da baturen ya ɓuya har aka damƙe shi.

Ƴan sanda sun faɗi laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa da suka kunshi ɗaukar nauyin ta'addanci, cin amanar ƙasa, laifukan intanet da haɗa baki wajen aikata miyagun laifuka.

Sai dai baturen ya fito ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, yana mai cewa bai ma da masaniyar an shafa masa baƙin fenti kuma ba a gayyace shi ba.

'Yan sanda ta musanta ikirarin Wynne

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a hedikwatar rundunar da ke Abuja, kakakin ƴan sanda Olumuyiwa Adejobi, ya ce sun gayyaci baturen sau da dama.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun jefa bama bamai a hedkwatar ƴan sanda, sun tafka ta'asa

Ya ce wanda ake zargin bai amsa ko ɗaya daga cikin gayyatar da aka tura masa ba har lokacin da jami'an ƴan sanda suka kai samame shagonsa.

"Mun gayyace shi sau da dama, mutum ne mara alƙibla, mun kai samame shagon da yake sayar da litattafai, amma ba mu same shi ba, har yanzun bai bayyana kansa ba."

Kakakin ƴan sandan ya ƙalubalanci Wynne da ya fito ya miƙa kansa ga doka kamar yadda wanda ake zarginsu tare ya yi idan har yana da gaskiya, Punch ta tattaro.

Bature ya musanta zargin da ake yi masa

A baya kun ji cewa Andrew Wynne, dan kasar Burtaniya da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta zarga da kokarin kifar da ita ya musanta zargin.

Mista Wynne ya bayyana cewa bai ma san ana neman shi ruwa a jallo bisa zargin yunkurin kawo sauyin gwamnati a Najeriya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262