"'Yan Bindiga Sun Shiga Uku": Gwamna Ya Sha Alwashi kan Matsalar Tsaro
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta ke addabar al'umma
- Sule ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da dukiyoyin ihar daga barazanar da ƴan bindiga ke yi
- Ya kuma buƙaci hukumomin tsaro su magance matsalar rashin tsaro inda ya yi alƙwarin ba su dukkanin goyon baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Gwamna Sule ya sha wannan alwashin ne sakamakon yawaitar sace-sacen jama’a musamman a sassan birnin Lafia, babban birnin jihar.
Wane alwashi gwamna Sule ya sha?
Gwamnan ya yi wannan alƙawarin ne bayan wata ganawa da ya yi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Ibrahim Addra ya fitar.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta bi duk hanyoyin da suka dace domin yaƙar barazanar da masu garkuwa da mutane, ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka ke yi a faɗin jihar.
Gwamna zai ba jami'an tsaro goyon baya
Gwamna Sule ya jaddada ƙudirinsa na bayar da cikakken goyon baya ga hukumomin tsaro, tare da ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, rahoton jaridar Thisday ya tabbatar.
Gwamnan ya bukaci hukumomin tsaron da su magance matsalar rashin zaman lafiya a ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Ya kuma nuna matuƙar damuwarsa kan yadda matsalar sace-sacen mutane ke ƙaruwa a birnin Lafia, inda ake garkuwa da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba domin neman kuɗin fansa.
Gwamna Sule ya goyi bayan Ganduje
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamman jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya gargaɗi ƴaƴan APC su bar shugaban jam'iyyar, Dr Abdullahi Umar Ganduje a mulki
Gwamna Sule ya yi kashedin cewa bai kamata ƴaƴan APC su raba hankalin Ganduje ba a daidai lokacin da jam'iyyar ke tunkarar zaɓen gwamna a jihohin Edo da Ondo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng