'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa, Sun Hallaka Shugaban Jam'iyya a Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa, Sun Hallaka Shugaban Jam'iyya a Jihar Arewa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun hallaka shugaban jam'iyyar adawa ta Labour Party (LP) na reshen jihar Benue
  • Ƴan bindigan sun hallaka Mista Sunday Oche wanda shi ne shugaban LP na Igumale a ƙaramar hukumar Ado
  • Marigayin ya rasa ransa ne bayan ƴan bindigan sun tare shi a hanya tare da wasu suna dawowa daga gona zuwa gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Ƴan bindiga sun hallaka wani shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) a jihar Benue.

Ƴan bindigan sun hallaka Mista Sunday Oche wanda shi ne shugaban jam'iyyar Labour Party a Igumale cikin ƙaramar hukumar Ado ta jihar Benue.

'Yan bindiga sun yi kisa a Benue
'Yan bindiga sun hallaka shugaban LP a jihar Benue Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka kashe shugaban LP

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kashe marigayin ne yayin wani kwanton ɓauna da suka yi masa a hnayar komawa gida.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari sakatariyar karamar hukuma, sun hallaka jami'an tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa ƴan bindigan sun yiwa marigayin kwanton ɓauna ne lokacin da yake dawowa daga gona a ranar Litinin, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

"Su shida ne suka je gonar a kan babura guda biyu. Suna kan hanyar dawowa wajen ƙarfe 4:30 sai ƴan bindigan suka yi musu kwanton ɓauna."
"Ƴan bindigan sun tare su inda nan take suka harbe shugaban jam'iyyar wanda shi ne suka fara tunkara. Harbin da suka yi masa ya sa ya mutu a wurin. Sauran mutum biyar ɗin sun samu sun tsira ɗauke da raunuka."

- Wata majiya

Me hukumomi suka ce kan harin?

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, sakataren yaɗa labaran Labour Party na jihar Benue, Tersoo Orbunde, ya bayyana cewa an ɗauko gawarsa inda yanzu ake jiran a binne shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun jefa bama bamai a hedkwatar ƴan sanda, sun tafka ta'asa

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, ta bayyana cewa ba ta samu rahoto kan lamarin ba.

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan sanda

A wani labarin kuma, kun ji wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun harbe ƴan sanda biyu da direba har lahira a Delta.

Maharan sun kashe ƴan sandan da ke tare da matar ɗan majalisar dokoki, Hon. Augustine Uroye, tare da direbanta, kana suka yi awon gaba da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng