'Yan Bindiga Sun Jikkata Matar Ɗan Majalisa, Sun Hallaka Ƴan Sanda a Najeriya

'Yan Bindiga Sun Jikkata Matar Ɗan Majalisa, Sun Hallaka Ƴan Sanda a Najeriya

  • Yan bindiga sun yi yunƙurin garkuwa da matar ɗan majalisar dokokin jihar Delta mai wakiltar Warri ta Kudu I, Hon Augustine Uroye
  • Bayanai sun nuna maharan sun harbe ƴan sanda biyu da ke tare da ita da direba, sun yi awon gaba da ita amma suka gamu da hatsari
  • Yanzu haka ne matar na kwance ana mata maganin raunukan da ta samu bayan ta tsere daga hannun maharan da suka yi hatsarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun harbe ƴan sanda biyu da direba har lahira a jihar Delta.

Maharan sun kashe ƴan sandan da ke tare da matar ɗan majalisar dokokin Delta, Hon. Augustine Uroye, tare da direbanta, kana suka yi awon gaba da ita.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun jefa bama bamai a hedkwatar ƴan sanda, sun tafka ta'asa

Taswirar jihar Delta.
Matar ɗan majalisa ta tsallake rijiya da baya a harin ƴan bindiga a Delta Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Matar ɗan majalisar mai wakiltar Warri ta Kudu I ta faɗa tarkon masu garkuwan ne ranar Litinin da daddare, kamar yadda Leadership ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 7:00 na dare a kan titin Jakpa da ke karamar hukumar Uvwie a jihar Delta.

Yadda matar ɗan majalisar ta kuɓuta

A rahoton Vanguard, wani ganau ya ce:

"Sun harbe jami'an tsaron da direban har lahira nan take daga bisani suka tafi da matar ɗan majalisar, Misis Christy Uroye.
"Amma maharan na cikin tafiya sai motarsu ta yi haɗari, hakan ya ba matar ɗan majalisar damar tserewa."

An tattaro cewa mutane sun kewaye wurin washe gari suna kallon ikon Allah, motar SUV da matar ke ciki da gawarwakin ƴan sanda da direban suna wurin a lokacin.

Wane hali matar ɗan majalisar ke ciki?

Rahotanni sun ƙara da cewa a halin yanzu matar ɗan majalisar na kwance a asibiti ana kula da lafiyarta bayan ta taki sa'a a harin da aka yi yunƙurin garkuwa da ita.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari kan matafiya, sun tafka ɓarna a Arewa

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Delta, SP Bright Edafe ta tabbatar da faruwar lamarin, inda aka ji tana cewa, "ba su cimma nasara ba,"

Mahara sun farmaki ƴan sanda a Anambra

A wani labarin kuma jami'i ɗaya ya mutu da ƴan bindiga suka kai mummunan farmaki a hedkwatar ƴan sanda da ke Oba a Anambra.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Tochukwu Ikenga ya ce maharan sun riƙa jefa bama-baman kwalabe a harin na safiyar Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262