"Ka Bi a Hankali": Gwamnan PDP Ya Gargadi Kwamishinan 'Yan Sanda
- Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara ya shawarci kwamishinan ƴan sandan jihar da ka da ya riƙa sanya siyasa cikin aikinsa
- Gwamna Fubara ya kuma gargaɗi ƴan sandan da ke marawa ƴan siyasa baya cewa za su yi da-na-sanin hakan nan gaba
- Fubara ya ba da wannan shawarar ne a wajen ƙaddamar da motoci 100 ta gwamnatinsa ta sayowa rundunar ƴan sanda
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya shawarci ƴan sandan da ke marawa wasu ƴan siyasa baya da su shiga taitayinsu.
Gwamna Fubara ya bayyana cewa ƙiyayyar da suke ƙoƙarin ƙara rura wutar ta, za ta yi musu illa a nan gaba.
Fubara ya ba da shawarar ne wajen ƙaddamar da sababbin motoci 100 da gwamnatinsa ta ba rundunar ƴan sandan jihar a filin wasa na Sharks da ke Port Harcourt ranar Talata, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara Gwamna Fubara ya ba da?
Jaridar The Punch ta ce kalaman gwamnan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi ya fitar.
"Ina buƙatar na gaya maka haka ta yadda za ka fahimta. Lokacin da aka kawo ka Rivers, kwamishina Tunji Disu na buƙaci abu ɗaya ne kawai a wajenka, shi ne ba zan taɓa cewa ka yi abin da bai da ce ba."
"Saboda haka ka yi abin da ya dace. Ka kare rayuka da dukiyoyin mutanen jihar Rivers. Ka da ka sanya siyasa a ciki."
"Mun ga yadda waɗanda suke sanya siyasa a cikin aikinsu yadda suka ƙare. Ina gayawa duk wanda yake a cikinku a nan wanda yake sanya siyasa a aikinsa, zai ga yadda ƙarshensa zai yi."
"Saboda haka, ku yi aiki ta yadda idan aka ambaci sunan ku a jihar nan, ko yaran ku suka zo jihar nan, ba za ku ji tsoro ba. Hakan yana da muhimmanci."
- Gwamna Siminalayi Fubara
Gwamna Fubara ya magantu kan ficewa PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara ya bayyana cewa yana nan daram a matsayin ɗan jam'iyyar PDP.
Gwamna Fubara ya faɗi hakan ne a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers lokacin da ya karɓi baƙuncin ƴan kwamitin amintattu na PDP (BoT).
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng