An Samu Matsala Tsakanin Tinubu da Shettima? Hadimin Kashim Ya Magantu
- An yi ta yada jita-jita cewa akwai matasala tsakanin Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima
- Sai dai fadar shugaban kasa ta yi magana kan rade-radin da yake yawo a yau inda ta ce babu gaskiya kan abin da ake yadawa
- Hadimin Shettima a bangaren sadarwa, Stanley Nkwocha shi ya bayyana haka inda ya ce akwai alaka mai kyau tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi magana kan rade-radin samun matsala tsakanin Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa.
Martanin na zuwa ne bayan zargin cewa alaka ta yi tsami tsakanin Mai girma Bola Tinubu da Kashim Shettima har ba a ga maciji.
Akwai matsala tsakanin Shettima da Tinubu?
Hadimin Shettima a bangaren yada labarai, Stanley Nkwocha ya ce akwai alaka mai kyau tsakanin Shettima da mai gidansa, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an kirkiri labarin ne kawai domin hada rigima inda ya ce kwata-kwata ba abin da ke faruwa ba kenan a Aso Rock.
Nkwocha ya karyata labarin da ake yadawa inda ya ce Shettima yana mutunta Tinubu matuka.
Hadimin Shettima ya fadi alakarsu da Tinubu
"Shettima ya himmatu wurin tabbatar da ba da goyon baya ga Bola Tinubu domin samun cigaba."
"Irin goyon baya da hadin kai da Shettima ke ba Tinubu shi ya kara daidaita tsakaninsu domin kawo sauyi a gwamnatinsu."
- Stanley Nkwocha
Stanley ya yabawa Shettima duba da irin hadin kai da ya ke ba shi inda ya ce Tinubu shugaba ne wanda 'yan Najeriya ya kamata su aminta da shi.
Ya shawarci al'umma da su guji yada jita-jita musamman irin wannan da zai kawo rudani a kasa.
Bikin ranar haihuwa: Shettima ya roki al'umma
Kun ji cewa Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ta roki yan Najeriya kan murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Sanata Kashim Shettima ya bukaci al'umma da su guji kashe kudi domin taya shi murnar cika shekaru 58 a duniya.
Mataimakin shugaban kasar ya bukaci masu son taya shi murnar su yi amfani da kudin wurin taimakon gidajen marayu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng