Gwamnati Ta Bayyana Adadin Litar Fetur da Matatar Dangote Za Ta Rika Samarwa a Kullum
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matatar man Dangote za ta rika samar da lita miliyan 25 na fetur a kullum a cikin watan Satumba
- Hukumar da ke sa ido kan harkokin man Najeriya (NMDPRA) ta ce matatar Dangote za ta kara yawan litar zuwa miliyan 30 a Oktoba
- Wannan na zuwa ne yayin da matatar man Dangote ta sanar da cewa ta shirya fitar da man fetur yayin da ta gabatar da samfurin man
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta ce matatar man Dangote za ta rika samar da lita miliyan 25 na fetur a kullum a watan Satumba.
Legit Hausa ta ruwaito cewa matatar Dangote ta sanar da fara samar da man yayin da ta gabatar da samfurin fetur din da ta tace.
Haka kuma ta kammala yarjejeniya da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) na sayar da danyen mai ga matatar Dangote a Naira, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yawan fetur da Dangote zai samar
Wannan ci gaban ya yi daidai da amincewar da majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta yi na sayar da danyen mai ga Dangote a Naira tare da sayen fetur daga matatar a kudin gidan.
“A hedikwatar NMDPRA da ke Abuja, NNPCL ta cimma yarjejeniyar fara sayar da danyen man fetur da kuma samarwa matatar man Dangote a cikin kudin gida.
“A watan Satumba, matatar za ta rika samar da lita miliyan 25 na fetur kullum a kasuwannin cikin gida. Daga nan za ta kara yawan zuwa lita miliyan 30 daga Oktoba."
- Inji hukumar NMDPRA, kamar yadda The Guardian ta rahoto.
Dangote ya yabawa gwamnati
Aliko Dangote, ya ce yarjejeniyar sayar da danyen man fetur ga matatarsa a Naira da Shugaba Bola Tinubu ya yi zai rage matsin lamba da ake fuskanta a musayar kudin waje.
Ya kuma nuna godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnatinsa bisa bullo da irin wannan dabarar da ya ce za ta kawo babban sauyi ga harkar mai a kasar.
NNPC ya kara kudin fetur
A yayin da 'yan Najeriya ke murna cewa matatar man Dangote za ta fara fitar da fetur da ta tace, kamfanin NNPCL ya kara kudin man daga N568 zuwa N855 har N897.
Mun ruwaito cewa karin farashin na zuwa ne awanni 48 bayan da kamfanin NNPC ya yi korafin cewa ya na bin wasu masu shigo da mai kasar bashin kudi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng