'Yan Bindiga Sun Jefa Bama Bamai a Hedkwatar Ƴan Sanda, Sun Tafka Ta'asa
- Jami'i ɗaya ya mutu da ƴan bindiga suka kai mummunan farmaki a hedkwatar ƴan sanda da ke garin Oba a jihar Anambra
- Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Tochukwu Ikenga ya ce maharan sun riƙa jefa bama-baman kwalabe a wannan harin
- Ya ce tuni jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji, ƴan sanda da sauran dakarun hukumomin tsaro suka fara farautar maharan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan aware ne sun kai hari hedikwatar ‘yan sanda da ke garin Oba karamar hukumar Idemili ta Kudu a Anambra.
Rahotannin da muka samu sun nuna cewa ƴan ta'addan sun kashe kofur na ƴan sanda a harin wanda suka kai da safiyar ranar Talata, 3 ga watan Satumba, 2024.
Mahara sun yi wa ƴan sanda ta'asa
Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa maharan sun kashe kofur tare da jikkata wasu jami'an ƴan sanda da ke aiki a hedikwatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ƙara da cewa ‘yan bindigar sun kuma kai hari a cibiyar Oba Civic Centre, har yanzu babu cikakken bayani kan dalilin kai wannan hari.
Amma harin ya zo a daidai lokacin da jagoron ƴan aware, Simon Ekpa, ya yi barazanar sa ƙafar wando ɗaya da duk wani abu da ya shafi gwamnati a Kudu Maso Gabas.
Ƴan sanda sun faɗi matakin da aka ɗauka
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da kai harin a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce tuni dakarun haɗin guiwa da suka kunshi, sojoji, jami'an tsaron fararen hula NSCDC da sauran hukumomin tsaro suka fara farautar maharan a Oba da Kewaye.
Kakakin ƴan sandan ya ce maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi da kuma jefa bama-baman kwalaben fetur a hedkwatar ƴan sandan, Punch ta kawo labarin.
"Abin takaicin kofur ɗaya wanda ya ji munanan raunuka a harin ya rasa ransa daga baya amma an yi nasarar kashe wutar da ta tashi da taimakon jami'an tsaro," in ji Ikenga.
Ƴan bindiga sun kai farmaki sakatariya a Anambra
A wani rahoton kun ji cewa wasu yan bindiga kimanin 30 sun dura ƙaramar hukumar Ogbaru a jihar Anambra inda suka bude wuta a sakatariya.
Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun yi kone kone a karamar hukumar kafin su yi musayar wuta da yan sandan jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng