An Shiga Alhini Bayan Sanar da Mutuwar Basarake Kuma Tsohon Sakataren Gwamnati
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi tsohon sakataren gwamnati, Michael Koleoso
- Makinde ya ce ya kadu da samun labarin mutuwar Koleoso inda ya ce tabbas an tafka babban rashi na mutumin kirki
- Marigayin kafin rasuwarsa ya rike mukarin sakataren gamnatin jihar daga shekarar 1999 zuwa 2003 a mulkin marigayi Lamidi Adesina
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Tsohon sakataren gwamnatin jihar Oyo, Michael Koleoso ya yi bankwana da duniya.
Marigayin ya rasu ne a jiya Litinin 2 ga watan Satumbar 2024 yana da shekaru 86 bayan ya sha fama da jinya.
Oyo: Tsohon sakataren gwamnati ya rasu
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da wakilin Punch ya samu a Ibadan a yau Talata 3 ga watan Satumbar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matigayin ya rike mukamin sakataren gwamnatin jihar Oyo a zamanin mulkin Lamidi Adesina.
Tribune ta ruwaito cewa marigayi tsohon gwamna Adesina ya yi mulki ne daga shekarar 1999 zuwa 2003.
Har ila yau, marigayin ya rike shugabancin tsohuwar jam'iyyar Alliance for Democracy (AD).
An zabi Koleoso a matsayin dan Majalisa a shekarar 1979 inda ya wakilci mazabar Ifedapo a jihar Oyo.
Gwamna ya tura sakon ta'azziya
Gwamna Seyi Makinde ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin inda ya ce an tafka babban rashi.
"Na kaɗu da samun labarin rasuwar Baba Michael Koleoso, tabbas al'ummar Oyo da Najeriya gaba daya sun yi babban rashi.
"Duk wadanda suka sanni sun san irin alakar da ke tsakaninmu, ina matukar mutunta shi, na dauke shi kamar uba."
- Seyi Makinde
Kwamishinan yan sanda ya rasu a Lagos
A wani labarin, kun ji cewa an shiga alhini bayan sanar da rasuwar Kwamishinan yan sanda na jihar Akwa Ibom.
Marigayi Waheed Ayilara ya rasu da safiyar ranar Alhamis 29 ga watan Agustan 2024 a asibitin koyarwa na Jami'ar Lagos
Wani babban dan sanda da ya bukaci boye sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana ba ya tabbatar da mutuwar Ayilara.
Asali: Legit.ng