Mahaifiyar Tsohon Shugaba Yar'Adua, Hajiya Dada Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Allah ya yiwa mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Umaru Musa Ƴar'adua rasuwa ranar Litinin, 2 ga watan Satumba, 2024
- Hajiya Dada Ƴar'adua ta riga mu gidan gaskiya a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Katsina (UMYUK) bayan fama da jinya
- Marigayyar ta kasance uwa ga Umaru Musa Yar'adua, marigayi Shehu Musa Yar'adua da Sanata Abdul'aziz, za a jananza gobe Talata bayan azahar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Umaru Musa Yar'adua, Hajiya Dada ta riga mu gidan gaskiya a jihar Ƙatsina.
Rahotanni sun nuna cewa Hajiya Dada ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya yau Litinin, 2 ga watan Satumba, 2024, tana da shekaru 102 a duniya.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa dattijuwar ta kwanta dama ne a asibitin koyarwa na jami'ar Umaru Musa Ƴar'adua (UMYUK) da ke cikin birnin Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hajiya Dada ta kasance mahaifiyar marigayi Shehu Musa Yar’adua da Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua, shugaban kwamitin kula da sojoji na majalisar dattawa.
Yaushe za a yi janazar Hajiya Dada Yar'adua?
Bayanan da muka samu sun nuna cewa za'ayi jana'izar ne a gidan iyalan 'Yar'adua da ke a cikin birnin Katsina da misalin karfe 1:30 na rana a gobe Talata.
Ta rasu ta bar ‘ya’ya da jikoki, daga cikinsu akwai Sanata mai wakiltar Katsina ta tsakiya a yanzu, Abdulazeez Musa Yar’adua.
Marigayi Umaru Musa Yar’adua ya zauna a kujerar shugaban ƙasa daga 2007 bayan ya ci zaɓe zuwa lokacin da Allah ya karɓi rayuwarsa a ranar 10 ga watan Mayu, 2010.
Ƴar'adua ya kuma riƙe kujerar gwamnan jihar Katsina na tsawon shekaru takwas, daga 1999 zuwa 2007, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Alkali Zailani ya rasu a Kaduna
A wani rahoton kuma kun ji cewa Allah ya yi wa tsohon Alkalin Alkalan jihar Kaduna, Mai shari’a Tanimu Zailani rasuwa a safiyar ranar Lahadi, 1 ga watan Agustan 2024.
Daya daga cikin iyalansa, kuma kakakin majalisar Kaduna ta tara, Yusuf Zailani ne ya sanar da rasuwar tsohon shugaban alkalan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng