Miyagun Ƴan Bindiga Sun Hallaka Babban Hadimin Shugaban Majalisa a Najeriya

Miyagun Ƴan Bindiga Sun Hallaka Babban Hadimin Shugaban Majalisa a Najeriya

  • Ƴan bindiga sun kashe Mista Samson Omoarebokhae, hadimin kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Rt. Hon. Blessing Agbebaku
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe matashin ɗan siyasar a hanyar zuwa Ozalla ranar Asabar, 31 ga watan Agusta, 2024
  • Kakakin majalisar ya aika tawaga ta musamman domin yiwa iyalan marigayin ta'aziyya tare da jajanta masu bisa wannan rashi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Rahotannin da muka samu sun nuna cewa wasu ƴan bindiga sun hallaka hadimin shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Samson Omoarebokhae.

Miyagun sun kashe Mista Omoarebokhae, babban mai taimakawa kakakin majalisar Edo na musamman, (SSA) ranar 31 ga watan Agusta, 2024.

Taswirar jihar Edo.
Yan bindiga sun kashe hadimin shugaban majalisar dokokin jihar Edo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa maharan sun yi ajalin ɗan siyasar a yayin da yake hanyar zuwa kauyen Uhomora daga Ozalla a ƙaramar hukumar Owan ta Yamma.

Kara karanta wannan

Kano: Dan majalisa zai taimaki addini, ya yi kyautar miliyoyin sayen motar wa'azi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar Edo ya yi ta'aziyya

Mai magana da yawun kakakin majalisar, Misis Ivy Adodo-Ebojele ce ta bayyana haka a wata sanarwar ta'aziyya ga iyalan marigayin ranar Litinin.

Ta ce bayan samun labarin lamarin, an tura tawaga karƙashin shugaban ma'aikatan kakakin majalisar, Mr Odion Iruobe, su je ta'aziyya har gida.

"Kakakin majalisar ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga majalisar, jam’iyyar PDP da karamar hukumar Owan ta Yamma,” in ji ta.

A saƙon da ya isar a madadin shugaban majalisar dokokin, Mista Iruobe ya buƙaci iyalan marigayi Omoarebokhae da su tuna cewa Allah ba zai bar su a cikin wannan jarabawa.

Wane mataki gwammatin Edo ta ɗauka?

Ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki domin doka ta yi aiki a kansu.

Dan uwan ​​mamacin, Mista Elijah Omoarebokhai, ya yabawa shugaban majalisar dokokin Edo bisa tura tawaga domin yi masu ta'aziyya, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kano: Dan Majalisar Tarayya ya warkar da makafi 3,000, Gwamna Abba ya yaba

Yan bindiga sun tare titi a Kogi

A wani rahoton kuma yan bindiga sun jikkata mafarauta da suka kai hari titin Takete Ide a karamar hukumar Mupamuro da ke jihar Kogi.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun tare matafiya, kuma sun kwace masu kuɗi da kayayyaki masu daraja a harin na ranar Lahadi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262