Sabuwar Zanga Zanga Ta Ɓarke a Abuja, Matasa Sun Aika Sako ga Shugaba Tinubu
- Zanga zanga ta sake ɓallewa a babban babban birnin tarayya Abuja kan karancin man fetur da ya ƙi ƙarewa a Najeriya
- Masu zanga-zangar sun nuna takaicinsu kan yadda lamarin ke ƙara lalacewa karƙashin shugaban kamfanin NNPCL
- Sun buƙaci Bola Ahmed Tinubu da sauran waɗanda ke riƙe da madafun iko su ɗauki mataki domin shawo kan lamarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Dandazon mutane sun fantsama kan tituna a babban birnin tarayya Abuja domin nuna fushinsu kan matsalar ƙarancin man fetur.
Masu zanga zangar sun bukaci a tsige shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) Mele Kyari, saboda ya gaza magance ƙarancin mai da aka jima ana fama da ita.
NNPCL ya koka kan ƙarancin kuɗi
Wannan zanga-zanga na zuwa ne bayan kamfanin NNPCL ya ce ɗumbin bashin da yake bin ƴan kasuwa na barazana ga wadatar mai Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A rahoton Punch, kamfanin ya ƙara da cewa ya fara shiga matsalar rashin isassun kuɗi wanda hakan ka iya daƙile ayyukansa da ƙarancin mai a ƙasa.
Yadda matasa suka yi zanga-zanga
Masu zanga-zangar sun riƙa rera waƙoƙin haɗin kai, sannan sun ɗaga kwalayen da aka rubuta, "mun gaji ƙarancin mai da surutu kan matatun mai," da sauransu.
Da yake jawabi ga manema labarai, jagoran masu zanga-zangar Aminu Abbas, ya ce yana mamakin yadda ake karancin mai a kasar da Allah ya azurta da albarkatun mai.
Ya kuma gargaɗi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da sauran masu rike da madafun iko su ɗauki mataki tun yanzu kafin abin ya sha ƙarfinsu.
Masu zanga-zanga sun aika saƙo
A rahoton Vanguard, Aminu Abbas ya ce:
"Shugaban ƙasa Bola Tinubu da sauran shugabanni, ya kamata ku tashi daga barci, lokaci ya yi da zaku ɗauki mataki, ku nuna mana kuna kishin talaka ba kishin aljihu ba.
"Muna wahala saboda ƙarancin mai, muna kokarin jurewa amma abin ba mai ƙarewa ba ne, ƙarƙashin Mele Kyari wahala kullun ƙaruwa take, babu alamar ƙarshe."
NNPCL na shirin miƙa matatu ga ƴan kasuwa
A wani rahoton kuma kamfanin man fetur na kasa ya fara neman yan kasuwa da za su iya rike wasu matatun man da ke karkashinsa.
Kamfanin NNPCL na neman yan kasuwar da za su iya kula da gyara matatun da ke Kaduna da Warri bayan sun gaza fara aiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng