Gwamna Radda Ya Dauki Mataki da Gobara Ta Tashi a Gidan Gwamnati

Gwamna Radda Ya Dauki Mataki da Gobara Ta Tashi a Gidan Gwamnati

  • Gwamnatin Katsina ta fara ɗaukar mataki kan tashin gobarar da aka samu a gidan gwamnati da aka fi sani da gidan Muhammadu Buhari
  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya kafa kwamitin da zai binciki musabbabin tashin gobarar tare da kura-kuran da suka haddasa ta
  • Kwamitin zai kuma ba da shawarwari kan hanyoyin kiyaye aukuwar gobarar sannan zai miƙa rahotonsa a cikin sati ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kafa kwamitin da zai binciki gobarar da ta auku a wani sashe na gidan gwamnatin jihar da aka fi sani da gidan Muhammadu Buhari ranar Litinin.

Gobarar ta lalata wani ɗaki da ke haɗe da ofishin gwamnan inda ya ke ganawa da manyan mutane.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Katsina, ta shafi bangaren ofishin gwamna

Gwamna ya kafa kwamitin bincike
Gwamna Radda ya kafa kwamitin bincike kan gobarar da ta tashi a gidan gwamnati Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Jami’an kashe gobara sun yi nasarar shawo kan gobarar kafin ta zarce zuwa wasu sassan ofishin, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Radda ya kafa kwamiti

Daily Trust ta ce sanarwar da daraktan yaɗa labarai na sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Yar’adua ya fitar a ranar Litinin, ta ce kwamitin yana da alhakin gano musabbabin tashin gobarar da kuma irin ɓarnar da ta yi.

"Kwamitin zai gano kura-kurai (idan akwai) waɗanda suka jawo aukuwar lamarin, ya ba da shawarar hanyoyin daƙile aukuwar lamarin nan gaba, tare da bayar da duk wata shawara mai muhimmanci."
"An ba kwamitin umarnin sanya duk wani mutum da zai taimaka musu wajen gudanar da aikinsu a cikinsa tare da miƙa rahoto a cikin sati ɗaya."

- Abdullahi Yar'adua

Su waye mambobin kwamitin?

Mambobin kwamitin sun haɗa da shugaban ma’aikatan gwamnati na jiha, kwamishinonin ayyuka, gidaje da sufuri, kasafin kuɗi da tsare-tsare, shari’a, tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, yaɗa labarai da al’adu.

Kara karanta wannan

Fasinjoji da dama sun bace yayin da jirgi ya kife a Bauchu

Sauran su ne babban sakatare na ɗaya na gidan gwamnati, kwamandan hukumar kashe gobara, yayin da ofishin gwamna zai samar da sakataren kwamitin.

Gwamna Radda ya faɗi hanyar dawo da tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi magana kan hanyar magance matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙasar nan.

A cewar gwamnan, idan har ana son magance matsalar tsaro, to akwai buƙatar magance matsalar iyakokin kasar tare da kawo karshen cin hanci da rashawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng