Likitoci Sun Dauki Mataki kan Yajin Aikin da Suka Shiga bayan Gargadin Gwamnati

Likitoci Sun Dauki Mataki kan Yajin Aikin da Suka Shiga bayan Gargadin Gwamnati

  • Kungiyar likitocin Najeriya masu neman sanin makamar aiki (NARD) ta sanar da janye yajin aikin kwanaki bakwai da suka shiga
  • A cikin wata sanarwar bayan taro da kungiyar ta fitar, NARD ta umarci 'ya'yanta da su koma bakin aiki daga ranar Litinin, 2 ga Satumba
  • Janye yajin aikin ya biyo bayan wani matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na kakaba tsarin 'ba aiki babu biyan albashi' ga likitocin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar likitocin Najeriya masu neman sanin makamar aiki (NARD) ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai da ta shiga.

Kungiyar ta fara yajin aikin ne a ranar Litinin 26 ga watan Agusta saboda ci gaba da zaman 'yar kungiyar, Dakta Ganiyat Popoola-Olawale a hannun 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Likitoci sun fadi abin da ke korarsu zuwa neman aiki a kasashen waje

Likitoci sun janye yajin aikin da suka shiga
NARD: Likitoci sun sanar da janye yajin aiki.
Asali: Twitter

Likitoci sun janye yajin aiki

Amma bayan taron majalisar zartarwarta (ENEC) da kungiyar ta gudanar a ranar Lahadi, 1 ga Satumba, 2024, kungiyar ta sanar da janye yajin aikin, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NARD ta ce ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne tare da sanya ido sosai kan abubuwan da ke faruwa, inda suka yi kira ga masu ruwa da tsaki da su sa baki a sako Dakta Ganiyat.

Sanarwar janye yajin aikin ta samu sa hannun shugaban kungiyar Dakta Dele Abdullahi Olaitan, babban sakatare, Dakta Anaduaka Christopher Obinna da sakataren jama'a, Dakta Egbe John Jonah.

Likitocin za su sake zama

A cewar sanarwar:

"Kungiyar NERD ta amince da cewa za a ci gaba da aiki a dukkan asibitocin da ke fadin kasar nan daga karfe 8:00 na safiyar ranar Litinin 2 ga Satumba, 2024."

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Gwamnatin Tinubu ta kakaba tsarin ba aiki ba biyan albashi, an samu bayanai

The Punch ta rahoto NARD ta ce majalisar zartarwata (NEC) ta kuma amince da sake zama nan da makonni uku domin sake tattaunawa kan lamarin.

Ta yaba da irin gudumawar da hukumomin gwamnati daban-daban suka yi, da kuma alkawarin da suka yi na kubutrar da likitar da aka sace.

'Babu aiki babu biyan albashi'

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kakaba tsarin 'ba aiki babu biyan albashi' kan kungiyar likitocin Najeriya masu neman sanin makamar aiki (NERD).

Ma’aikatar lafiya da jin dadin jama’a ta tarayya ce ta kakaba tsarin, tana mai cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga lafiyar 'yan kasa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.