Gobara Ta Tashi a Gidan Gwamnatin Katsina, Ta Shafi Bangaren Ofishin Gwamna

Gobara Ta Tashi a Gidan Gwamnatin Katsina, Ta Shafi Bangaren Ofishin Gwamna

  • Rahotanni sun nuna cewa gobara ta kama wani sashe na gidan gwamnatin jihar Katsina a safiyar yau Litinin, 2 ga watan Agustan 2024
  • Har yanzu dai ba a tantance musabbabin tashin wutar ba a yayin da hukumomi ke kokarin kashe kashe gobarar da ake zargin ta yi barna
  • An rahoto cewa Gwamna Dikko Umaru Radda na a karamar hukumar Funtua inda ya ke halartar wani taro a lokacin da gobarar ta afku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Rahotanni sun bayyana cewa wata gobara ta tashi da sanyin safiyar yau Litinin, 2 ga watan Satumba a gidan gwamnatin jihar Katsina.

An ruwaito cewa bangaren da gobarar ta kama ya na hade ne da ofishin gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda, inda ya ke ganawa da manyan mutane.

Kara karanta wannan

An fara shari'ar masu zanga zanga, za su iya fuskantar hukuncin kisa a kotu

Gobara ta tashi a gidan gwamnatin jihar Katsina
Katsina: Gobara ta tashi a wani bangare na gidan gwamnati. Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Katsina

Jaridar Leadership ta ta ruwaito cewa babu wani tabbaci kan musabbabin tashin gobarar da kuma irin barnar da ta yi a lokacin wannan rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai an ce hukumar kashe gobara da sauran hukumomin da abin ya shafa na ta kokarin ganin an kashe gobarar wadda ake fargabar ta lalata dukiyoyi masu muhimmanci.

Gwamna Dikko Radda yana Funtua

An tattaro cewa Gwamna Dikko Umaru Radda ya na a karamar hukumar Funtua inda ya ke halartar taron shiyyar a lokacin da gobarar ta afku, inji rahoton Daily Trust.

An ce ya halarci taron ne domin tattaunawa da jama'ar shiyyar game da bukatunsu da kuma abin da suke fatan gwamnatin ta yi masu.

Gobara ta kone ofishin gwamna

A wani labarin, mun ruwaito cewa gobara ta tashi a ofishin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a safiyar ranar Talata, 12 ga watan Disambar shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Zamfara: Gwamna ya ba da tallafin kudi da filaye ga wadanda ambaliya ta shafa

Rahoto ya nuna cewa Gwamna Zulum na a dayan ofishinsa da ke sakatariyar Musa Usman lokacin da gobarar ta tashi a dayan ofishin da misalin karfe 12:30 na rana.

Rundunar yan sanda sun hana motoci, ma’aikata da manema labarai shiga gidan gwamnatin yayin da 'yan kwana kwana ke kokarin kashe gobarar da ta tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.