"Ka Yi Daidai": Shekarau Ya Yabawa Tinubu kan Nade Nade, Ya Fadi Damuwar Arewa

"Ka Yi Daidai": Shekarau Ya Yabawa Tinubu kan Nade Nade, Ya Fadi Damuwar Arewa

  • Tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya yabawa Bola Tinubu kan nadin shugabannin hukumomin tsaro daga yankinsa
  • Sanata Shekarau ya ce Tinubu ya yi dai dai da ya nada hafsoshin tsaron kasar daga yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
  • Tsohon gwamnan ya ce damuwar Arewa shi ne wanda aka nadan idan zai samar da cigaba shi ne babban abin da ake bukata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya yi magana kan nadin shugabannin tsaro.

Shekarau ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan nadin shugabannin tsaro daga yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Shekarau ya yabi Tinubu kan nadin mukamai
Ibrahim Shekarau ya fadi damuwar Arewacin Najeriya a gwamnatin Bola Tinubu. Hoto: Mallam Ibrahim Shekarau, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Shekarau ya yabi Tinubu kan mukamai

Kara karanta wannan

"Sai an dage": Sule Lamido ya yi magana kan yiwuwar kifar da Tinubu a 2027

Sanata Shekarau ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar Punch ta wayar tarho a yau Lahadi 1 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya ce kowa Tinubu ya nada mukami idan har zai samar da abin da ake bukata abin yabawa ne.

Ya ce kungiyarsu ta League of Northern Democrats da ya ke jagoranta ba ta damu da hakan ba idan har za a samu abin da ake bukata.

"Kalubale ne ga yankin Arewacin Najeriya amma ba abin damuwa ba ne idan har kwararru ne kuma za su iya."
"Idan har duka mukaman daga Lagos suke, ba za mu damu ba, damuwarmu shi ne cigaban Arewa, duk wanda aka nadan shin zai iya yin aikin.?'

- Ibrahim Shekarau

Shekarau ya fadi abin da Buhari ya yi

Shekarau ya ce tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi haka inda ya nada hafsoshin tsaro daga Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana zargin abubuwa 2 suka tilasta murabus din shugaban hukumomin DSS da NIA

"A baya, Buhari ya yi haka lokacin da ya nada hafsan sojoji da daraktan DSS da na NIA da hafsan sojojin sama da kuma babban sifetan 'yan sanda daga Arewa."

- Ibrahim Shekarau

Shekarau ya tuno wahalar da ya sha

Kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya fadi irin kalubalen da ya fuskanta a siyasa.

Shekarau ya ce a zaben gwamnan Kano a 2003 sai da ya nemi bashin kudi domin siyan fom din takara kan N5m.

Shekarau ya bayyana haka ne yayin taron lakca na tunawa da marigayi Danbatta inda ya ce ba zai taba mantawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.