An yi rashi a Kaduna: Tsohon Shugaban Alkalai, Tanimu Zailani Ya Kwanta Dama

An yi rashi a Kaduna: Tsohon Shugaban Alkalai, Tanimu Zailani Ya Kwanta Dama

  • Allah ya yi wa tsohon Alkalin Alkalan jihar Kaduna, Mai shari’a Tanimu Zailani rasuwa a safiyar ranar Lahadi, 1 ga watan Agustan 2024
  • Daya daga cikin iyalansa, kuma kakakin majalisar Kaduna ta 9, Yusuf Zailani ne ya sanar da rasuwar tsohon shugaban alkalan
  • Hon. Yusuf Ibrahim Zailani ya bayyana cewa za a jana'izar "mahaifinmu" da misalin karfe 1 na rana a gidansa da ke Rigachikun, Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban alkalan jihar Kaduna, Mai shari'a Tanimu Zailani ya kwanta dama.

Kamar yadda labarin rasuwarsa ya riske mu, an ce Mai shari'a Tanimu ya rasu ne a safiyar Lahadi a Kaduna bayan gajeriyar jinya.

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Jerin manyan sarakunan gargajiya na Najeriya da suka rasu a 2024

Allah ya yiwa tsohon shugaban alkalan Kaduna, Tanimu Zailani rasuwa
Tsohon alkalin alkalan Kaduna, Mai shari'a Tanimu Zailani ya rasu. Hoto: @SpeakerZailani
Asali: Twitter

Mai shari'a Zailani ya rasu

Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna na 9, Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani ya wallafa sanarwar rasuwar tsohon shugaban alkalan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rt. Yusuf Zailani ya sanar da cewa:

"Ina mai alhinin sanar da ku cewa Allah ya karbi rayuwar mahaifinmu, Mai shari'a Tanimu Zailani, tsohon shugaban alkalan jihar Kaduna.
"Za a yi jana'izarsa a gidansa da ke Rigachikun da misalin karfe 1 na rana. Muna addu'ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya ba mu ikon jure rashinsa."

Kadan daga rayuwar alkalin

Mai shari’a Zailani shi ne shugaban sashin shari’a na jihar Kaduna, da kuma bangaren shari’a na gwamnatin Kaduna.

Haka zalika marigayin ya rike mukaminbabban alkalin babbar kotun Kaduna daga shekarar 2013 zuwa 2018, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.

Bayan ritayar Mai shari'a Zailani ne aka nada Mai shari'a Muhammadu Lawal Bello a matsayin sabon shugaban alkalan Kaduna.

Kara karanta wannan

An shiga alhini bayan sanar da rasuwar fitaccen jarumin fina-finai a Najeriya

Uwar gidan Sarki Shehu ta rasu

A wani labarin daga jihar Kaduna, mun ruwaito cewa uwar gidan marigayi Alhaji Shehu Idris, tsohon sarkin Zazzau, Hajiya Habiba ta rigamu gidan gaskiya.

An ruwaito cewa Hajiya Habiba Shehu Idris, wadda suruka ce ga sarkin Zazzau na yanzu, Alhaji Nuhu Bamalli ta rasu ne a safiyar ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.