Iyalin Tsohon Shugaban Alkalai na Najeriya sun rasu a hadarin mota

Iyalin Tsohon Shugaban Alkalai na Najeriya sun rasu a hadarin mota

- Tsohon Alkalin Alkalai Mahmood Muhammad ya rasa Uwargidar sa jiya

- Hadarin mota ya kashe Iyalin na babban Alkalin yayin da wasu ke jinya

- Tuni an birne Uwargidar ta sa a Masallacin Titin Yahaya a cikin Kaduna

Mun samu labari cewa Matar Tsohon Shugaban Alkalai gaba daya na Najeriya Mahmood Muhammad sun rasu a wani mummunan hadarin mota tsakanin Birnin Tarayya Abuja zuwa Garin Kaduna wanda tuni har an birne su a Kaduna.

Iyalin Tsohon Shugaban Alkalai na Najeriya sun rasu a hadarin mota
An birne Iyalin Mahmood Muhammad a Masallacin Unguwan Rimi

Tsohon Alkalin Kotun Kolin kasar nan Mahmood Muhammad ya rasa Uwargidar sa ne a wani hadarin mota jiya. Kamar yadda daya daga cikin Iyalin babban Alkalin Kasar mai suna Baballiya Aftaka ya bayyana dai tuni Direban motan ya rasu.

KU KARANTA:

Ban da dai Direban motar watau Alhaji Abdurra’uf, Uwargidan tsohon babban Alkalin na Najeriya watau Hajiya Hadiza Mahmood Muhammad ita ma ta cika. ‘Dayar Matar sa watau Hajiya Hauwa Mahmood Muhammad tana asibiti a halin yanzu.

Haka kuma Hajiya Lami Atiku wata ‘Yar uwar daya daga cikin Matan wannan Bawan Allah tana asibiti inda su ka samu mugun rauni. Tuni dai har an yi jana’izar wannan Direba da kuma Uwargidar tsohon babban Alkalin Kasar a cikin Kaduna.

Haka kuma dai a jiya daya daga cikin manyan Limaman Masallacin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya Dr. Mustafa Qasim ya rasa daya daga cikin matan sa. Wannan Baiwar Allah tayi ta fama da rashin lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng