Shugaba Bola Tinubu Ya Isa Kasar China, Bidiyo Ya Bayyana
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka ƙasar China cikin nasara a ziyarar aikin da ya je gudanarwa
- Shugaba Tinubu ya isa birnin Beijing na China a ranar Lahadi, 1 ga watan Satumban 2024 inda zai halarci tarurruka masu muhimmanci
- A yayin ziyarar ta sa a China, Shugaba Tinubu zai tattauna da Shugaba Xi Jinping tare da shugabannin manyan kamfanunnika a ƙasar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Kasar China - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa ƙasar China domin yin ziyarar aiki.
Shugaba Tinubu ya isa birnin Beijing na ƙasar China ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Satumban 2024.
Tinubu ya isa ƙasar China
Hadimin Tinubu kan kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun ne, ya bayyana hakan a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu a yayin zamansa a ƙasar China, zai halarci taron Afirika da China karo na tara da za a gudanar a ƙasar.
"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Beijing a ziyarar aiki da yaje a ƙasar China."
"Zai gana da Shugaba Xi Jinping kuma zai yi tarurruka da shugabannin ɓangarorin kasuwanci na China bayan taron Afirika da China."
- Dada Olusegun
Tinubu ya amsa gayyatar Shugaban China
Tun da farko Shugaba Xi Jinping na ƙasar China ya gayyaci Tinubu ya ziyarci ƙasar a watan Satumba.
A cewar fadar shugaban ƙasa, ana sa ran ziyarar za ta ƙara bunƙasa dangantakar tattalin arziƙi a tsakanin ƙasashen biyu da jawo masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.
Shugaba Tinubu zai ziyarci manyan ƙamfanoni a China irin su kamfanin Huawei Technologies da 'China Railway and Construction Corporation' domin sanyawa a kammala aikin ɓangaren titin jirgin ƙasa na Ibadan-Abuja a titin jirgin ƙasan da ya taso daga Lagos zuwa Kano.
An buƙaci Tinubu ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa matasan ƙabilar Ijaw a ƙarƙashin ƙungiyar Ijaw Youth Council (IYC), sun buƙaci Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi murabus daga muƙamin ministan man fetur.
Matasan sun buƙaci Shugaba Tinubu ya naɗa tsayayyen wanda zai ci gaba da jagorantar ma'aikatar bayan ya yi murabus ɗin.
Asali: Legit.ng