Sarautar Kano: Aminu Ado ya Kaddamar da Fara Sabunta Fadar Nassarawa, an Yada Hotuna
- Yayin da ake cigaba da rigimar sarautar Kano, Sarkin jihar na 15, Aminu Ado Bayero ya fara sabunta masarautar Nassarawa
- An ruwaito cewa Aminu Ado ya fara fadada fadar daga ciki inda ake sa ran bayan kammalawa zai inganta wajen masarautar
- An wallafa hotunan zanen yadda fadar za ta kasance duk da korafi kan basaraken da cewa tubabben sarki ne a jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya kaddamar da fara sabunta masarautar Nassarawa.
Wannan mataki na Sarkin ya dauki hankulan jama'a yayin da ake cigaba da rigimar masarautu.
Kano: Aminu Ado ya fara gyara fadarsa
Leadership ta wallafa wasu hotunan da aka zana domin fara garambawul a masarautar da Aminu Ado Bayero ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu na ganin wannan mataki ya nuna himmatuwar Sarkin na cigaba da kasancewa a kujerar sarauta.
Hakan ya biyo bayan tuge Sarkin daga sarautar jihar wanda Gwamna Abba Kabir ya yi bayan hawa karagar mulki.
Dan morin Kano kuma na kusa da Aminu Ado mai suna Hassan Abubakar ya tabbatar da fara ginin masarautar.
Hassan ya ce Sarkin ya fara fadada masarautar daga ciki inda ya ce yanzu haka ana kan aikin.
Ya ce bayan kammala gyaran cikin masarautar, Sarkin ya shirya sabunta wajen fadar tare da kuma mashigarta.
Har ila yau, Hassan ya ce basaraken yana gyaran ne da kudin aljihunsa ba tare da wani ya taimaka masa da sisin kwabo ba.
Kalli hotunan sabuwar fadar Nassarawa a kasa:
Kano: Aminu Ado ya kai ziyara Abuja
Kun ji cewa A karon farko bayan ɓarkewar rikicin sarauta, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi tafiya zuwa wajen jihar Kano.
Basaraken wanda ya koma Kano a watan Mayu, 2024 bayan an sauke shi daga sarauta, ya fita daga jihar zuwa babban birnin Tarayya da ke Abuja.
Wata majiya ta ce sarkin ya tafi wata ziyarar aiki ne zuwa Abuja domin halartar wani babban taro da aka gayyaci sarakuna da dama a kasar.
Asali: Legit.ng