Mutuwar Yunusa Danyaya: Gwamnan Bauchi Ya Sanar da Nada Sabon Sarkin Ningi na 17
- Gwamnatin jihar Bauchi ta ayyana Alhaji Haruna Yunusa Danyaya a matsayin sabon sarkin Ningi domin ya gaji mahaifinsa, marigayi alhaji Yunusa
- Wata sanarwa daga mai ba gwamnan Bauchi shawara kan watsa labarai, Mukhtar Gidado, ta bayyana cewa Alhaji Haruna zai zama sarki na 17
- An ce Gwamna Bala Mohammed ya amince da nadin Alhaji Haruna Danyaya bayan shawarar masu nadin sarki da kuma amfani da ikonsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da nadin Alhaji Haruna Yunusa Danyaya a matsayin Sarkin Ningi.
Rahotanni sun bayyana cewa Alhaji Haruna shi ne babban da ga marigayi Alhaji Yunusa Danyaya, kuma shi ne zai zama sarkin Ningi na 17.
An nasa sabon sarkin Ningi
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai ba Gwamna Bala shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Kwamared Mukhtar Muhammad Gidado ya sanar da hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamared Mukhtar ya bayyana cewa:
"An yi nadin nadin ne bisa shawarar masu nadin sarki da kuma amfani da karfin ikon sashe na 24, bangare na 3 (1) na dokar Bauchin Najeriya (nada sarakunan gargajiya da sauke su ta 1991).
“An mika nadin ne a wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Bauchi Barista Ibrahim Muhammad Kashim."
Gwanna ya karfafi sabon sarki
Sanarwar wadda Legit Hausa ta gani ta kara da cewa:
"Gwamnatin Bauchi ta na da yakinin cewa sabon sarkin zai dora daga inda mahaifinsa (mai rasuwa) ya bari na hada kan jama, wanzar da zaman lafiya da ci gaban masarautar Ningi."
Sanarwar ta ce gwamnati za ta ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa masarautun gargajiya a jihar domin rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban al’ummarmu.
Gwamna Bala ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayi Alhaji Yunusa Danyaya, ya kuma ba sabon sarkin lafiya da nisan kwana a wa'adin mulkinsa.
Sanarwar ta ruwaito cewa an haifi sabon Sarkin Ningi Alhaji Haruna Yunusa Danyaya, a shekarar 1956. Shi ne ciroman Ningi kafin a nada shi sarki.
Ana murna da nadin Haruna
A zantawarmu da Musa Mohammed Ningi, wani dan jarida daga jihar Bauchi, ya bayyana cewa al'ummar Ningi na murnar da wannan nadin na Alhaji Haruna Yunusa Danyaya.
Musa Ningi ya ce a tsawon zamansa Ciroman Ningi, alhaji Haruna ya nuna shi mai tausayi talakawa ne kuma mai kokarin ganin an samu zaman lafiya ne da kaunar juna.
Dan jaridar ya rahoto cewa tun bayan sanar da sabon sarkin aka dauki shewa a Ningi, domin ana ganin Gwamna Bala Mohammed ya ajiye kwarya a burminta.
Sarkin Ningi ya kwanta dama
A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya yiwa Alhaji Yunusa Danyaya, sarkin masarautar Ningi na 16 rasuwa bayan ya yi fama da rashin lafiya.
An ce marigayi mai martaba Sarki Yunusa ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi 25 ga watan Agustan 2024 a wani asibiti da ke Kano, inda ake kula da lafiyarsa.
Asali: Legit.ng