Gwamnan Bankin CBN Ya Sallami Manyan Daraktoci daga Aiki, an Jero Dalilai

Gwamnan Bankin CBN Ya Sallami Manyan Daraktoci daga Aiki, an Jero Dalilai

  • Wasu daraktoci a Babban Bankin CBN sun rasa mukamansu bayan gwamnan bankin ya amince da sallamarsu
  • Olayemi Cardoso ya amince da korar manyan daraktocin ne karkashin hukumar NIRSAL da ke ba da basuka
  • Wannan na zuwa ne yayin da bankin CBN ke kokarin kawo gyara a sha'anin gudanar da harkokinsa cikin shekara daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sallami wasu manyan daraktoci daga mukamansu a karshen wannan mako da muke ciki.

Bankin ya dakatar da daraktocin ne da ke jagorantar NIRSAL da su ke ba da tallafi da basuka ga 'yan Najeriya.

Bankin CBN ya kori manyan daraktoci daga mukamansu
Gwamnan bankin CBN ya kori wasu manyan daraktocin NIRSLA. Hoto: Central Bank of Nigeria.
Asali: Facebook

CBN ya sallami manyan daraktocinsa a Abuja

Kara karanta wannan

Hankula sun kwanta da sojoji suka fadi lokacin dakile matsalar tsaro, an samu cigaba

Leadership ta tattaro cewa daga cikin daraktocin akwai babban darakta, Abbas Umar Masanawa da daraktan ayyuka, Kennedy Nwaruh da kuma daraktan fasaha, Olatunde Akande.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani jami'i a ofishin NIRSAL ya tabbatar da haka inda ya ce wadanda ke karkashinsu suna sauraron karin bayani kan korar daraktocin.

Wannan na zuwa ne yayin da CBN ke korarin kawo sauye-sauye a bankin wanda ake ganin shi ne musabbabin sallamar daraktocin.

Gwamnan bankin CBN ya amince da korarsu

Premium Times ta ce matakin ya samu sahalaewar gwamnan CBN, Olayemi Cardoso a ranar Juma'a 29 ga watan Agustan 2024.

Wata majiya a bankin ta ce daukar matakin ya jefa tsoro a zukatan manyan ma'aikata har ma kanana kan abin da ka iya biyo baya.

Rahotannin sun tabbatar da cewa tun bayan hawan Cardoso mukami cikin shekara daya an sallami ma'aikata sun kai 700 a kokarin da ake yi na sauye-sauye.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: CBN ya fadawa 'yan Najeriya gaskiyar halin da za a shiga

Tsadar rayuwa: CBN ta gargadi 'yan Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da rahoto kan barazanar da take fuskantar yan Najeriya.

CBN ya nuna cewa cikin watanni masu zuwa yan Najeriya da dama za su shiga ƙarancin kudi wajen biyan bukatunsu na yau da kullum.

Babban Bankin CBN ya yi hasashen cewa nan da watanni masu zuwa al'umma da dama za su fuskanci ƙarancin kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.