'Yan Bindiga Na Kai Hare Hare, Gwamnan Sokoto Ya Gargadi 'Yan Adawa
- Gwamnan jihar Sokoto ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta daɗe tana ciwa jihar tuwo a ƙwarya
- Gwamna Ahmed Aliyu ya gargaɗi masu siyasantar da matsalar rashin tsaron da su shiga taitayinsu su daina aikata hakan
- Gwamnan ya nuna cewa matsalar rashin tsaro abu ne da ya shafi kowa saboda haka ba zai lamunci wasu su siyasantar da lamarin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya gargaɗi mutane ko ƙungiyoyi da su daina siyasantar da matsalar tsaro a jihar.
Gargaɗin na gwamnan na zuwa ne yayin da matsalar tsaro a jihar ke ƙara taɓarɓarewa sakamakon ayyukan ƴan bindiga.
Gwamna Ahmed Aliyu ya yi wannan gargaɗin ne a wata ziyara da ya kai ƙaramar hukumar Goronyo a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me gwamnan Sokoto ya ce kan rashin tsaro?
Gwamnan ya yi kira da a guji yin kalaman da za su iya kawo tashin hankali dangane da matsalar rashin tsaron.
"Tsaro abu ne mai muhimmanci da ya shafe mu baki ɗaya, kuma ba za mu lamunci duk wani yunƙuri na amfani da shi domin cimma wata manufa ta siyasa ba."
"Saboda haka, ina kira ga kowa da kowa da a guji yin kalamai masu kaushi ko kuma ɗaukar matakan da za su kawo cikas ga zaman lafiyar mutane ba."
"Ba za mu amince da duk wani mai ƙoƙarin sanya siyasa a harkokin tsaro ba, kuma za mu ɗauki matakan da suka dace domin hana irin waɗannan ayyukan kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharmu."
- Gwamna Ahmed Aliyu
Ya buƙaci jama'a da su kai rahoto kan abubuwan zargi ko mutanen da ba a yarda da su ba wajen hukumomin da suka dace tare da yin aiki tare domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Sokoto.
An cafke hadimin Tambuwal a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta gurfanar da hadimin Sanata Aminu Tambuwal kan cin zarafin gwamnan jihar.
Ana zargin Shafi'u Tureta da cin mutuncin Gwamna Ahmed Aliyu inda ya wallafa faifan bidiyo da cewa bai iya yaren Turanci ba ko kaɗan.
Asali: Legit.ng