An Shiga Jimami a Kano, Gini Ya Danne Mata Da ’Ya’yanta Ana Tsaka da Tafka Ruwan Sama

An Shiga Jimami a Kano, Gini Ya Danne Mata Da ’Ya’yanta Ana Tsaka da Tafka Ruwan Sama

  • An samu wani mummunan lamari da ya kai ga mutuwar wata mata da gini ya danne a wani yankin jihar Kano
  • Rahoto ya bayyana cewa, a halin yanzu ‘ya’yanta biyu na can asibitin Murtala Muhammad suna karbar magani
  • Mazauna yankin sun bayyana yadda ginin ya fadi da kuma yadda aka ceto wadannan bayin Allah a birnin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kano - Wani iftila’i ya auku a unguwar Makwarari da ke jihar Kano a ranar Juma’a, lokacin da wani gini ya ruguje, inda ya kashe wata mata mai shekaru 35, Balaraba Tijjani tare da raunata ‘ya’yanta biyu.

An tattaro cewa, ginin ya ruguje ne bayan da aka tafka ruwan sama a yankin, wanda ya fara tun ranar Alhamis da dare har safiyar Juma’a.

A cewar mazauna yankin, matar da ‘ya’yanta biyu; Abdulnasir da Abdallah masu shekaru 11 da 13 bi da bi a yanzu haka suna asibiti Murtala Muhammad da ke birnin.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya ja kunnen jami’ai, an karyata zancen saida filin masallacin idi

Yadda gini ya danne wata mata da 'ya'yanta a Kano
Yadda gini ya danne wata mata da 'ya'yanta a jihar Kano | An saka hoton nan ne don buga misali da rugujewar gini, ba ainihin in da lamarin ya auku bane a Kano
Asali: Getty Images

Allah ya dauki matar da gini ya danne

Sai dai, abin takaici an rasa mahaifiyarsu a yayin da aka yi gaggawar tafiya da ita tare da yaran zuwa asibitin, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wani mazaunin yankin:

“Bayan ceto wadanda ginin ya dannen, an gaggauta tafiya dasu asibitin kwararru na Murtala Muhammad. Sai dai, an yi rashin sa’a raunuka sun cimma Balaraba wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta, amma ‘ya’yanta na ci gaba da karbar magani.”

Hukumar kashe gobara ta yi bayani

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar, kakakin rundunar hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi ya ce ginin ya rushe ne da misalin karfe 9:30 na safe ranar Juma’a, Solace Base ta tattaro.

A cewarsa:

“Saboda haka, ginin ya danne mutane uku, uwa Balaraba Abba mai shekaru 35 da kuma ‘ya’yanta biyu Abdulnasir Jilani mai shekaru 12 da kuma Abdullahi Jilani mai shekaru 9.

Kara karanta wannan

Kwalliya ta zo da gardama: Budurwa ta sheka lahira a wajen tiyatar karin mazaunai

“Tare da kokarin mazauna yankin, an yi nasarar ceto wadanda ginin ya danne kuma an kai su asibitin Murtala Muhammad a lokacin da jami’an hukumarmu suka iso.”

Wani gini ya fadi a Kano

A wani labarin na daban, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce har yanzu ma'aikata na aikin zakulo wadanda gini ya rufta musu a Kano.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, SFS Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatarwa Legit Hausa cewa yanzu haka ana ta aikin ceton rai, kuma babu tabbacin adadin wadanda su ka rasu.

Ya kara da cewa jami'ansu da sauran jami'ai na ci gaba da kokarin zakulo wadanda ginin ya ruftawa domin ceton rai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.