A Kawo Dauki, an Yi Kutse a Shafin Facebook Na Hisbah, Ana Ta Yada Bidiyon Batsa

A Kawo Dauki, an Yi Kutse a Shafin Facebook Na Hisbah, Ana Ta Yada Bidiyon Batsa

  • Shafin Facebook na hukumar Hisbah a jihar Kano ya koma hannun wasu masu yada abubuwan batsa a shafukan intanet
  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ana ci gaba da kokarin tabbatar da dawo da shafin
  • Sani Zailani, wani jami’i a Hisbah ya tofa albarkacin bakinsa kan kokarin da ake yi waje kwato shafin hukumar

Jihar Kano - Wasu tsageru sun yi kutse tare da kwace mallakar shafin Facebook na hukumar Hisbah ta jihar Kano, inda suka yi ta yada bidiyo da hotunan batsa.

Lamarin da ya auku tun ranar Larabar da ta gabata na ci gaba da daukar hankalin jama’a tare da tofin Alla-tsine a shafukan sada zumunta.

Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar juma’a, inda yace hukumar na kokarin shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

"Muna kan aiki," Gwamna ya faɗi matakin da ya ɗauka kan biyan sabon albashin N70,000

An kwace asusun Facebook na Hisbah
An kwace asusun Hisbah a kafar Facebook | Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Bayanin Sheilk Daurawa a madadin Hisbah

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta san da kwace mallakin shafinta na Facebook da kuma yada munanan abubuwa. A madadin Hisbah, muna kira ga jama’a da su taimaka a warware matsalar.”

Ya kuma tabbatarwa al’umma cewa, sashen sadarwa da fasaha na hukumar na yin ruwa da tsaki wajen tabbatar da an dawo da shafin hannun hukumar, rahoton Punch.

Hakazalika, ya kuma yi kira ga al’umma da su kai karar shafin ga kamfanin Meta cikin harshen turanci don dakile ci gaba da yada abubuwan batsa a shafin.

Ba wannan ne karon farko da kwace shafin Hisbah ba

Sani Zailani, wanda shi ne shugaban sashen sadarwa da fasaha na Hisbah, ya ce shafin ya taba fuskantar irin wannan lamari, kuma an gaggauta warware hakan cikin sa’o’i 48.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya ja kunnen jami’ai, an karyata zancen saida filin masallacin idi

Sani ya kuma yabawa al’umma da suka ankarar da hukumar tare da kokarin da suke wajen ganin an dawo da shafin hannun Hisbah.

Ba sabon abu bane a Najeriya samun yadda mutane ke kwashe mallakar shafukan sada zumunta, wanda ke zama barazana ga jama’a.

Hisbah ta kwace basara a Katsina

A wani labarin, Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta ƙwace kimanin katan 142 na barasa da aka shirya kaiwa ƙaramar hukumar Daura.

Kwamandan Hisbah na jihar, Dakta Aminu Usman ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Katsina ranar Asabar.

A cewar Aminu Usman, an kama barasar ne a ranar Litinin a yayin wani sintiri a faɗin birnin domin kawar da munanan ɗabi'u da rashin ɗa'a, cewar rahoton jaridar The Guardian.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.