Ministar Tinubu Ta Sake Wargaza Taro, Ta Koka kan Rainata da Aka Yi, Ta Yi Gargadi a Bidiyo
- Ministar mata a Najeriya, Uju Kennedy-Ohanenye ta wargaza wani gagarumin taro da ake yi a birnin Tarayya Abuja
- Kennedy-Ohanenye ta koka kan yadda aka shirya taron ba tare da saninta ba inda ta ce za ta dauki mummunan mataki
- Ministar ta nuna damuwa kan yadda ake barnar kudi a irin wannan taruka musamman a wannan hali da ake ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministar mata a Abuja ta sake ba mutane mamaki yayin da ta kai ziyara wurin wani taro.
Uju Kennedy-Ohanenye ta shiga taron bazata inda ta wargaza jama'a saboda an shirya ba da saninta ba.
Ministar Tinubu ta tarwatsa taro a Abuja
The Cable ta tattaro cewa Kennedy-Ohanenye ta koka kan yadda aka shirya taron inda ta ce ana kashe kudi babu wani dalili.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa ma'aikatar mata a Abuja ce ta shirya taron da kuma hadin guiwar matan Majalisar Dinkin Duniya, cewar Punch.
Ministar ta ja kunnen ma'aikatar inda ta ce dole ne daga yanzu a rika sanar da ita duk wani taro da za a yi.
Minista ta koka kan halin kunci
"Wannan ya zama na karshe da za a shirya taro a ma'aikatar mata ba tare da sani na ba, idan kuka yi haka a gaba zan zo na ci mutuncinku."
"Na san abin da ake ciki a wannan kasa, wannan shi ne abin da za mu rika yi da kuma shiryawa."
"Makwanni kadan da suka wuce an yi zanga-zangar halin kunci da rashin tsaro ga shi an bar mata babu sana'a."
"Amma duk da matsalolin da ake da su, an zo ana kashe kudi a banza, mutane da yawa ba za su fahimce ni ba, kuma a shirye nake da koma mene za a ce."
- Uju Kennedy-Ohanenye
Minista ta janye korafi kan kakakin Majalisa
Kun ji cewa Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta janye ƙorafin da ta shigar a kotu kan kakakin Majalisar Niger, Abdulmalik Sarkin-Daji.
Ministar ta dauki matakin ne kan shirin aurar da mata marayu 100 a jihar Niger da Sarkin-Daji ya shirya daukar nauyi.
Uju ta bayyana haka ne a ranar Juma'a 17 ga watan Mayu inda ta ce sun yi haɗaka da Majalisar jihar da sarakuna a jihar domin gudanar da bincike.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng