Ma'aikata Za Su Warwasa, Gwamna a Arewa Ya Shirya Biyan Sabon Albashin N70,000

Ma'aikata Za Su Warwasa, Gwamna a Arewa Ya Shirya Biyan Sabon Albashin N70,000

  • Gwamna Nasir Idris ya yi alƙwari da zaran an kammala tsara komai, zai fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi a Kebbi
  • Nasir Idris Kauran Gwandu ya ce gwamnatinsa ta shirya fara biyan sabon albashin ba kamar yadda wasu ke yaɗawa ba
  • Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da kungiyar kwadago NLC ta kai masa ziyara har gidan gwamnatinsa da ke Birnin Kebbi yau Jumu'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Ma'aikatan gwamnatin jihar Kebbi za su dara yayin da Gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya ce ya gama shirin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta fara biyan N70,000 da aka amince a matsayin albashin ma'aikata mafi ƙaranci.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Matakan da aka ɗauka a taron gwamnatin Tinubu da ASUU sun bayyana

Gwamna Nasir Idris.
Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Asali: Twitter

Daily Trust ta ce gwamnan ya faɗi hakan ne a Birnin Kebbi ranar Juma’a lokacin da shugabannin kungiyar kwadago NLC suka kai masa ziyara a gidan gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kebbi ta shirya fara biyan N70,000

Ya ce ya samu labarin cewa wasu mutane sun fara yawo suna yaɗa labarin ƙanzon kurege cewa gwamnatinsa ba za ta iya biyan sabon albashin ba.

Gwamna Nasir ya yi wa ma'aikatan alƙawarin cewa da zaran an kawo tsarin yadda za a biya sabon albashin, zai fara biya ba tare da ɓata lokaci ba.

"Hatta gwamnatin tarayya da ta amince da sabon albashin ba ta fara biya ba. Dole sai an bi wasu matakai kafin a fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashin.
"Da zaran an shirya, gwamnati na da ƴan kwadago za su zauna su tattauna kan yadda za a aiwatar da dokar sabon albashin," in ji shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya yiwa fitaccen mawakin siyasa kyautar sabuwar mota, ya saki bidiyo

NLC ta yabawa gwamnan Kebbi

Gwamnan ya ƙara da cewa harajin N500 da aka saba cirewa tun tuni, shi ne dai gwamnatinsa take cirewa daga albashin kowane ma'aikaci a shekara, Sahara Reporters ta tattaro labarin nan.

Tun da farko shugaban NLC na jihar, Kwamared Murtala Usman, ya ce sun kawo ziyarar ne domin nuna jin daɗinsu da jinjina ga mai girma gwamnan wanda ya kasance abokin ma'aikata.

Yobe ta musanta amincewa da biyan N70,000

A wani rahoton kuma gwamnatin jihar Yobe ta yi magana kan maganganun da ke nuna cewa da amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Gwamnatin a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta musanta cewa ta amince da sabon mafi ƙarancin albashin na ma'aikata a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262