Zanga Zanga Ta Barke kan Cin Zarafin ’Yan Matan Shi’a a Abuja, Bayanai Sun Fito

Zanga Zanga Ta Barke kan Cin Zarafin ’Yan Matan Shi’a a Abuja, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan cire hijabin wasu mata 'yan shi'a, yan kungiyar sun gudanar da zanga-zanga a Abuja
  • Masu zanga-zangar wadanda mafi yawansu mata ne sun fito domin nuna damuwa kan cin zarafin 'yan sandan
  • Hakan ya biyo bayan kwamishinan 'yan sandan birnin tarayya Abuja ya ce ba za a sake ganin zanga-zangar 'yan shi'a ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Daruruwan 'yan shi'a ne suka fantsama titunan Abuja domin nuna rashin jin dadi kan cin zarafinsu.

Yan kungiyar sun nuna damuwa kan yadda yan sanda suka cirewa mambobinsu mata hijabi a Abuja.

Yan Shi'a sun fara zanga zanga a Abuja
Zanga Zanga ta barke a Abuja kan cin zarafin matansu. Hoto: Legit.
Asali: Original

'Yan Shi'a sun yin zanga-zanga a Abuja

Kara karanta wannan

"Za mu saka kafar wando daya da ku": Majalisar Tarayya ta ja kunnen al'umma

AIT ta wallafa faifan bidiyon da yan shi'an ke zanga-zanga wanda mafi yawansu mata ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata mai suna Fatima Ibrahim, mai magana da yawun masu zanga-zangar ta caccaki jami'an tsaro kan lamarin.

Fatima ta ce hijabi addini ne da al'ada kuma 'yancinsu ne wanda bai kamata a ci zarafinsa ba.

Ta ce tube musu hijabi da cin zarafinsu yafi zafi a gare su fiye da harbinsu da alburusai.

Mabiya Shi'a sun koka kan cin zarafinsu

"Mun zo nan ne domin fadawa jami'an tsaro cewa mun yi Allah wadai da abin da suka aikata."
"Muna son fadawa dukan Musulman duniya su yi duba ga wannan abu da yan sanda suka aikata."
"Hijabi dokar Allah ne wanda ya halicci sammai da kasai kuma ubangijin talikai."

- Fatima Ibrahim

Boko Haram sun farmaki 'yan Shi'a

A wani labarin, kun ji cewa wasu yan ta'adda da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kan makarantar Shi'a ta Faudiyya a Yobe.

Kara karanta wannan

Malaman addini sun samo dabara, an nemowa Tinubu hanyoyin rage tsadar abinci

Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addar sun kai hari ne cikin dare a lokacin da dalibai ke cikin barci a makarantarsu da ke jihar.

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a makarantar Faudiyya da ke karamar hukumar Geidam kuma an samu harasar rayuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.