Ana Kan Zargi Game da Kujerarsa, Basarake Lamba 1 Ya Daga Darajar Sarakuna 6

Ana Kan Zargi Game da Kujerarsa, Basarake Lamba 1 Ya Daga Darajar Sarakuna 6

  • Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Akinloye Olakulehin ya yi karin girma ga wasu sarakuna har guda shida da ke karkashinsa
  • Oba Olakulehin ya yi karin girman ne ga sarakunan a fadarsa da ke Ibadan a yau Alhamis 29 ga watan Agustan 2024
  • Daga cikinsu akwai Oba Tajudden Abimbola daga Otun Balogun zuwa Balogun na Ibadan sai kuma Oba Kolawole Adegbola zuwa Otun Balogun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Fitaccen basarake a jihar Oyo, Olubadan na Ibadan ya daga darajar wasu sarakuna guda shida.

Oba Owolabi Akinloye Olakulehin ya dauki matakin ne a fadarsa gaban kwamitin masarautar da jami'an gwamnati.

Olubadan ya yi karin girma ga sarakuna 6
Olubadan na Ibadan a Oyo, Oba Owolabi Olakulehin ya karawa sarakuna 6 girma. Hoto: Oba Owolabi Akinloye Olakulehin.
Asali: Facebook

Olubadan ya yi karin girma ga sarakuna

Kara karanta wannan

Kotu ta dakatar da Gwamna cigaba da rushe shagunan kasuwa, ta gindaya sharuda

Daga cikin wadanda suka shaida karin girma ga sarakunan sun hada da iyalan basaraken, Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olubadan ya daga darajar Oba Tajudden Abimbola daga Otun Balogun zuwa Balogun na Ibadan, cewar Leadership.

Sai kuma Oba Kolawole Adegbola daga Asipa Balogun zuwa Otun Balogun na Ibadan sai Oba John Olubunmi daga Ekerin Balogun zuwa Osi Balogun na Ibadan.

Sauran sun hada da Oba Dauda Abiodun daga Ekerin Balogun zuwa Asipa Balogun sai Cif Akeem Bolaji daga Abese zuwa Ekerin Balogun sai Sharafadden Abiodun daga Maye Balogun zuwa Ekarun Balogun na Ibadan.

An gudanar da tsarin tabbatar da su a gargajiyance wanda Oluwo na Ibadan ya gudanar yayin da aka karrama su da ganyen Akoko.

Ana zargin Gwamna Makinde kan tsarin masarautu

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Gwamna Seyi Makinde ya sauya dokar masarautun jihar saboda wata manufa.

Kara karanta wannan

Kwanaki 4 da mutuwar basarake mai daraja ta 1, masu neman sarauta 5 za su fafata

Wasu na zargin gwamnan ya yi hakan ne saboda hana mai gadon kujerar Olubadan na Ibadan samunta cikin sauki a nan gaba.

Olubadan: Ladoja ya sha alwashin darewa karaga

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja ya yi magana kan neman sarautar Olubadan mai daraja a jihar.

Ladoja ya ce idan yana raye babu wanda zai hana shi darewa sarautar Olubadan komai daren dadewa a jihar.

Tsohon gwamnan ya amince da karbar sandan sarauta ta musamman a matsayin wani mataki na zama Olubadan a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.