Yajin Aiki: Gwamna a Arewa Ya Fara Lallaɓa Malaman Jami'a, Ya Masu Tayin N947m

Yajin Aiki: Gwamna a Arewa Ya Fara Lallaɓa Malaman Jami'a, Ya Masu Tayin N947m

  • Gwamna ya yi wa malaman jami'ar Gombe alƙawarin biyan alawus-alawus ɗin da suka biyo bashi domin ka da su shiga yajin aiki
  • Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa za ta fitar da N947,669,909.13 domin biyan alawus din a taron majalisar zartaswa na ranar Litinin
  • Wannan yunƙuri na gwamnatin Gombe na zuwa a lokacin da ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki saboda rashin cika alƙawari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe - Gwamna Inuwa Yahaya ya roki kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen jihar Gombe ta haƙura da shiga yajin aiki.

Gwamma Inuwa Yahaya ya yi wannan rokon ne a lokacin da ya karɓi bakuncin tawagar ƙungiyar ASUU ta jami'ar jihar Gombe (GSU) a gidan gwammati ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

"Muna kan aiki," Gwamna ya faɗi matakin da ya ɗauka kan biyan sabon albashin N70,000

Muhammad Inuwa Yahaya.
Gwamnatin Gombe ya fara kokarin lallaba ASUU ta haƙura da shiga yajin aiki Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Sakataren gwamnatin jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Njodi shi ne ya wakilci gwamnan yayin ziyarar ASUU, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya ɗaukarwa ASUU alƙawari

Gwamnan ya yi alƙawarin biyan alawus-alawus ɗin malaman jami'a na N947,669,909.13 daga nan zuwa ranar Monday domin lallaɓa su kada su shiga yajin aiki.

A cewar gwamnan, bayan taron majalisar zartaswa ranar Litinin mai zuwa, ba za a sake jin ɗuriyar ASUU za ta shiga yajin aiki a jihar Gombe ba.

Inuwa Yahaya ya ƙara da cewa matuƙar gwamnatinsa ba ta biya kuɗin daga nan zuwa Litinin ba, ya amince malaman jami'ar su ɗauki duk matakin da suka ga dama.

Inuwa Yahaya zai biya ASUU haƙƙoƙinsu

"A taron majalisar zartaswa na ranar Litinin, za a amince da fitar da N947,669,909.13 domin biyan alawus-alawus din malaman jami'a da bashin da suka biyo na ƙarin girma."

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta ƙara jiƙawa Ganduje aiki kan korar wasu shugabannin APC

"Abin da nake fata shi ne ASUU ta yi hakuri. Maganar tafiya yajin aiki a yanzu kamar yadda mai gabatarwa ya faɗa ba zai magance wata matsala ba."

- Gwamna Inuwa Yahaya.

Da yake jawabi tun da farko, Farfesa Daniel Gongula, wanda ya jagoranci tawagar ASUU reshen Gomɓe, ya yaba wa gwamnan bisa yadda ya ba da fifiko ga ilimi, rahoton Tribune.

Gwamnatin Tinubu ta fara lallaɓa ASUU

Kuna da labarin gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar matakan shawo kan kungiyar ASUU bayan ta yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya.

A taron da suka yi ranar Laraba, gwamnati ta hannun ma'aikatar ilimi ta kafa kwamiti da zai sake nazarin bukatun ASUU.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262