An Tono Abin da Shugaban Kwadago Ya Fada wa Yan Sanda da Suka Gayyace Shi

An Tono Abin da Shugaban Kwadago Ya Fada wa Yan Sanda da Suka Gayyace Shi

  • Bayanai sun fito kan abubuwan da shugaban kwadago ya tattauna da yan sanda bayan ya amsa gayyatarsu a ranar Alhamis
  • An ruwaito cewa zaman ya karkata ne kan wani mai shago da yake zaman haya a sakatariyar yan kwadago a Abuja
  • Rundunar yan sandan Najeriya ta gayyaci Joe Ajaero ne domin amsa tambayoyi kan zargin ta'addanci da cin amanar kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An samu bayanai kan abin da shugaban kwadago ya tattauna da yan sanda yayin da ya amsa gayyatar su.

Rahotanni sun nuna cewa Joe Ajaero ya kusa fusata a zaman a lokacin da yan sanda suke kiransa da sunansa ba tare da haɗawa da matsayinsa ba.

Kara karanta wannan

"Zargin N432bn: Nasir El Rufai ya fadi babbar matsalar cigaban siyasa

Yan kwadago
Abin da shugaban kwadago ya fadawa yan sanda. Hoto: @NLCheadquaters, @PoliceNG
Asali: Twitter

Rahoton Vanguard ya nuna cewa zaman ya mayar da hankali ne kan wani mutum da yake sakatariyar yan kwadago.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gayyatar shugaban yan kwadago

An gano cewa yan sanda sun gayyaci shugaban kwadago ne domin amsa tambayoyi a kan mai shagon sayar da littafi na Iva Valley Bookshop.

Mai shagon Iva Valley Bookshop ya kasance yana zaman haya ne a sakatariyar yan kwadago da ke birnin tarayya Abuja.

Me Joe Ajaero ya fada wa yan sanda?

Yayin da yan sanda ke yiwa shugaban yan kwadago tambayoyi, Joe Ajaero ya ce ba shi da wata alaƙa da mutumin sai ta mai gida da mai haya.

The Sun ta wallafa cwa Joe Ajaero ya ce mutumin ba ya neman shawarar NLC kuma ba wata alaƙa ta zance ko ta waya ko a rubuce a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

An harbe ƙasurgumin ɗan bindiga da ya sace manyan mutane a Najeriya

Ajaero ya fusata yayin zama da yan sanda

Wanda ya halarci zaman ya ce Joe Ajaero ya fusata yayin da yan sanda suke kiransa da sunansa ba tare da haɗawa da shugaban kwadago ba.

An ruwaito cewa zaman an yi shi cikin girmamawa kuma bai wuce tsawon mintuna 30 ba.

Maganar Ajaero bayan ganawa da yan sanda

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kungiyar kwadagon NLC, Joe Ajaero ya yi jawabi bayan barin ofishin rundunar yan sandan Najeriya a Abuja.

Joe Ajaero ya ce babu gudu babu ja da baya kan ƙoƙarin inganta rayuwar ma'aikata a faɗin Najeriya a kowane lokaci hakan ya taso.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng