Yan Bindiga Kimanin 30 Sun Dura Karamar Hukuma, Sun Cinna Wuta da Harbe Harbe

Yan Bindiga Kimanin 30 Sun Dura Karamar Hukuma, Sun Cinna Wuta da Harbe Harbe

  • Wasu yan bindiga kimanin 30 sun dura ƙaramar hukumar Ogbaru a jihar Anambra inda suka bude wuta a sakatariya
  • Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun yi kone kone a karamar hukumar kafin su yi musayar wuta da yan sandan jihar
  • Rundunar yan sandan Anambra ta fitar da bayani kan halin da ake ciki a Ogbaru bayan ta fatattaki yan bindigar zuwa dazuka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra - Yan bindiga sun yi ƙawanya a sakatariyar ƙaramar hukumar Ogbaru da ke jihar Anambra.

An ruwaito cewa yan bindigar wanda yawansu ya kai 30 sun dura ƙaramar hukumar ne da asuba inda suka fara ta'addanci.

Kara karanta wannan

Boko Haram ta kai hari kan yan Shi'a, an harbe mutane har lahira

Yan bindiga
Yan bindiga sun kai hari Anambra. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kakakin yan sanda a jihar ya yi karin haske ga manema labarai kan halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun dura ƙaramar hukuma

Rahotanni sun nuna cewa wasu yan bindiga su kusan 30 sun kai hari sakatariyar ƙaramar hukumar Ogbaru da misalin karfe 5:00 na safe.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa yan bindigar sun fito ne daga maboyarsu suna ihu suna harbe harbe.

Barnar yan bindiga a karamar hukumar

Vanguard ta ruwaito cewa yan bindigar sun cinna wuta a ofisoshi da dakin taro a sakatariyar karamar hukumar.

Haka zalika sun fara kone kone a wasu gine gine kafin zuwan jami'an tsaro su nufo wajen su fara musayar wuta.

Yan sanda sun fatattaki yan bindigan

Bayan yan bindiga sun fara barna ne yan sanda suka isa wajen suka fatattakesu kuma daga nan suka koma maboyarsu.

Kara karanta wannan

Fargaba a Abuja: 'Yan bindiga sun harbe magidanci, sun sace matarsa da yaransu

Kakakin yan sanda a jihar Anambra, Tochukwu Ikenga ya ce ba a samu hasarar rayuka ba amma an lalata wurare kuma hakan ya jawo asarar dukiya.

An kai hari kan yan Shi'a a Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa wasu yan ta'adda da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kan yan kungiyar Shi'a a jihar Yobe da ke Arewacin Najeriya.

Bayanai sun tabbatar da cewa yan ta'addar sun kai hari ne makarantar Faudiyya a ƙaramar hukumar Geidam yayin da dalibai ke barci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng