Kotu Ta Dakatar da Gwamna Cigaba da Rushe Shagunan Kasuwa, Ta Gindaya Sharuda
- Babbar kotun Imo ta dakatar da gwamnatin jihar daga koshirin rushe babbar kasuwar Owerri da ke jihar
- Alkalin kotun, C. Ibeawuchi shi ya yanke hukuncin a jiya Alhamis 29 ga watan Agustan 2024 a Owerri
- Wannan na zuwa ne yayin da Gwamna Uzodinma ke kokarin rushe kasuwar bayan korar wadansu daga cikinta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Imo - Babbar kotun jihar Imo ta yi hukunci kan rushe ginin kasuwa da gwamnatin ke shirin yi.
Kotun ta umarci Gwamna Hope Uzodinma ya dakatar da shirinsa na rushe shaguna a babbar kasuwar Owerri da ke jihar Imo.
Rusau: Kotu ta dakatar da gwamnan Imo
Alkalin kotun, I. C. Ibeawuchi shi ya yanke hukuncin a jiya Alhamis 29 ga watan Agustan 2024, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibeawuchi ya kuma umarci Gwamna Uzodinma da wasu mutane guda biyar da su dakatar da daukar duk wani mataki kan lamarin.
Kotun ta kuma dakatar da cigaba da gina katangar kasuwar har sai bayan zaman kotun da kuma matakin da ta dauka.
Imo: Lauyan masu kara ya yi tsokaci
Lauyan masu kara, Christian Nwadigo ya ce wadanda ke korafin sun hada da Incorporated Board of Trustees of Rhema Life Ministry International da Sunway Global Properties Limited.
Sai kuma Zero-one Global Properties Limited da Ekpereamaka Nwankwo da kuma Nwankwo Emmanuel, Punch ta tattaro.
Nwadigo ya ce masu korafi suna bukatar kotun ta dawo musu da kadarorinsu da aka kwace tare da biyansu diyya.
Zanga-zanga: Kotu ta yi hukunci a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan korafin da aka shigar da masu zanga-zanga a Najeriya.
Kotun ta yi fatali da korafin bayan wadanda suka shigar da korafin su 17 ba su halarci zaman kotun ba da aka gudanar a ranar Alhamis 29 ga watan Agusta.
Alkalin kotun, Peter Lifu ne ya yanke hukuncin bayan kin halartar kotun da suka yi duba da kin tura wani lauya da zai wakilce su a zaman kotun da aka yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng