Fargaba a Abuja: 'Yan Bindiga Sun Harbe Magidanci, Sun Sace Matarsa da Yaransu

Fargaba a Abuja: 'Yan Bindiga Sun Harbe Magidanci, Sun Sace Matarsa da Yaransu

  • Rahotanni da suka fito daga birnin tarayya Abuja sun nuna cewa yan bindiga sun kai mummunan hari yankin Ushafa a Bwari
  • An gano cewa yan bindigar sun harbe wani magidanci har lahira kuma sun samu nasarar tafiya da wasu daga cikin iyalansa
  • Mazauna yankin sun bayyanawa manema labarai cewa yan bindigar sun yi dirar miƙiya gidan mutumin ne a daren Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yan bindiga sun kai mummunan hari a yankin Ushafa da ke Bwari a birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun kai mummunan harin ne a daren Alhamis, 29 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

An harbe ƙasurgumin ɗan bindiga da ya sace manyan mutane a Najeriya

Abuja
Yan bindiga sun kashe magidanci a Abuja. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an samu harasar rai na wani magidanci yayin harin da yan ta'addar suka kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun harbe magidanci a Abuja

Rahotanni da suka fito daga birnin tarayya Abuja sun nuna cewa yan bindiga sun kai hari yankin Ushafa a daren Alhamis.

Punch ta wallafa cewa bayan bude wuta da yan bindigar suka yi a yankin, sun kutsa gidan wani mutum inda suka kashe shi har lahira.

'Yan bindiga sun sace matar aure da yara

Bayanai sun nuna cewa yan bindigar sun tafi da matar mutumin bayan sun hallaka shi a cikin daren Alhamis.

Dadin dadawa, rahotanni sun tabbatar da cewa miyagun yan bindigar sun tattare ƴaƴan mutumin sun tafi da su.

Yan sandan Abuja sun tabbatar da kashe magidanci

Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa lamarin ya faru sai dai ba ta yi karin haske sosai a kan harin ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kwanton bauna a kauye, sun budewa shugaban tsaro wuta

Manema labarai sun yi kokarin tuntubar kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh amma ba ta amsa waya ba.

Yan bindiga sun kai hari a Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Anambra na nuni da cewa yan bindiga sun mamaye wani kauye kuma suka harbi shugaban tsaron garin.

Mummunan lamarin ya faru ne a yankin Obosi a karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra kamar yadda bayanai suka tabbatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng