Bayan Gaza Tayar da Matatun Man Najeriya, NNPCL na Neman Mika Su ga 'Yan Kasuwa

Bayan Gaza Tayar da Matatun Man Najeriya, NNPCL na Neman Mika Su ga 'Yan Kasuwa

  • Kamfanin man fetur na kasa ya fara neman yan kasuwa da za su iya rike wasu matatun man da ke karkashinsa
  • NNPCL na neman yan kasuwar da za su iya kula da gyara matatun da ke Kaduna da Warri bayan sun gaza fara aiki
  • Kamfanin ya ce ya na bukatar kamfanonin da ke da kwarewa domin ba shi amanar matatun gwamnatin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya fara neman kamfanonin da za su iya kula da wasu daga cikin matatun man da ake da su a kasar nan.

Kara karanta wannan

Magani na gagarar talaka: Masu ciwon sukari sun nemi alfarma wajen Shugaba Tinubu

Lamarin na zuwa a lokacin da fetur ke kara karanci da tsada, wanda ke kara jawo tsadar kayan amfanin yau da kullum.

NNPCL
Kamfanin NNPCL na neman yan kasuwa su kula da matatun fetur din Kaduna da Owerri Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

A tallan neman kamfanonin da za su iya aikin a shafinsa na Facebook, kamfanin NNPCL ya ce za a mika harkar kula da matatu biyu na kasar nan ga yan kasuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanne matatun za a ba yan kasuwa?

Kamfanin NNPCL na son mika matatun fetur guda biyu domin inganta aikinsu wajen samar da man fetur ga yan Najeriya, NNPCL ya wallafa a shafinsa na X.

Matatun man da ke cikin tsarin sun hada da matatar fetur ta Kaduna da daya matatar da ke Warri.

Yan kasuwa za su farfado da matatun?

Wani mai sharhi kan al'amuran fetur kuma dan kungiyar IPMAN da ya nemi a sakaye sunansa ya ce batun mika matatun fetur ga yan kasuwa na da sarkakiya.

Kara karanta wannan

NiMET: Jerin jihohin Arewa 6 da za a tafka ruwa da iska mai karfi, an gargadi mutane

Ya shaidawa Legit cewa zuwa yanzu, matatar Dangote na fuskantar barazana kuma har yanzu ba ta fara abin da ake bukata ba, ballantana wasu kamfanonin.

An zargi NNPCL kan tallafi fetur

A baya kun ji cewa an samu karuwar masu zargin kamfanin mai na kasa (NNPCL) da nuku-nuku kan batun dawo da tallafin man fetur da shugaba Bola Tinubu ya cire.

A kalaman tsohon sakataren gudanarwan kungiyar NEITI, Waziri Adio ya ce akwai bukatar kamfanin NNPCL ya gaggauta fitowa da bayanai dalla-dalla kan batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.