Mutanen Gari Sun Yi Fito Na Fito da 'Yan Bindiga, Sun Hallaka Miyagu Masu Yawa
- Mutanen ƙauyen Matusgi da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara sun cire tsoro sun tunkari ƴan bindiga
- Mutanen bayan sun yi fito na fito da miyagun ƴan bindigan, sun samu nasarar hallaka mutum 37 daga cikinsu har lahira
- Hakimin ƙauyen wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa mutanen ƙauyen mutum uku sun rasa ransu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Mutanen gari sun hallaka aƙalla ƴan bindiga 37 a ƙauyen Matusgi a ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.
Mutanen sun samu nasarar ne bayan sun yi fito na fito da ƴan bindigan waɗanda suka farmaki ƙauyen da niyyar sace mutane.
Yadda aka hallaka ƴan bindigan
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa ƴan bindigan sun shigo ƙauyen ne a kan babura da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce ba wannan ba ne karo na farko da mutanen ƙauyen suka yi fito na fito da ƴan bindigan, amma shi ne karo na farko da suka yi musu ɓarna mai yawa.
Ƴan bindigan suna shiga ƙauyen sai suka fara harbi kan mai uwa da wabi domin su firgita mutane. Sai dai mutanen sun san da zuwansu inda suka yi shiri na musamman kafin su iso.
Bayan kwashe awa ɗaya ana musayar wuta, ƴan bindigan sun ja da baya bayan an kashe musu mutum 10. Daga nan sai mutanen suka sake taruwa suka yi musu kwanton ɓauna.
Lokacin da ƴan bindigan suka dawo sai mutanen ƙauyen suka sake farmakarsu inda suka kashe musu jimillar mutum 37, rahoton DCL Hausa ya tabbatar.
An tabbatar da aukuwar lamarin a Zamfara
Hakimin Matusgi, Alhaji Ciroma Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an kashe mutanen ƙauyen mutum uku.
Ya bayyana cewa mutanen da ke zaune a ƙauyukan da ke makwabtaka da su sun ga ƴan bindigan suna ɗauke da gawawwakin mutanensu da aka hallaka a kan babura.
Mutane sun tashi tsaye
Wani mazaunin jihar Zamfara, Jamilu Abdullahi, ya shaidawa Legit Hausa cewa tuni mutane suka fara ɗaukar matakin kare kansu saboda gwamnati ta gaza wajen samar da tsaro.
Ya bayyana cewa wurare da dama a jihar Zamfara sun ɗauki matakan kare kansu daga ta'addancin da ƴan bindiga ke tafkawa.
"Wannan abin da suka yi abin a yaba ne domin gwamnati ta kasa yin abin da ya dace domin magance matsalar. Ba zai yiwu mutane su zauna suna kallo ƴan bindiga na ci musu mutunci yadda suka ga dama ba."
- Jamilu Abdullahi
Sojoji sun hallaka wasu ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun hallaka wasu da ake zargin ƴan binidiga ne mutum biyu a jihar Kaduna a Arewa maso Yamma.
Sojojin sun kuma cafke wani mai ba su bayanai a ƙauyen Kurmin-Kare cikin ƙaramar hukumar Kachia ta jihar bayan sun bi sawunsa cikin kasuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng