Zanga Zanga: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Karar da Aka Shigar da Matasa, Ta Jero Dalilai

Zanga Zanga: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Karar da Aka Shigar da Matasa, Ta Jero Dalilai

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi zama kan korafin da aka yi game da masu zanga-zangar matsin tattalin arziki
  • Kotun ta kori karar saboda rashin halartar wadanda suka shigar da kara su 17 a gabanta a zaman da aka yi a yau Alhamis
  • Alkalin kotun ya yi fatali da karar ganin cewa babu wani daga cikin masu korafin da ya zo ko turo lauya da zai wakilce su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan korafin da aka shigar da masu zanga-zanga a Najeriya.

Kotun ta yi fatali da korafin bayan wadanda suka shigar da korafin su 17 ba su halarci zaman kotun ba.

Kara karanta wannan

Hankula sun kwanta da sojoji suka fadi lokacin dakile matsalar tsaro, an samu cigaba

Kotu ta yi hukunci kan karar da aka shigar da masu zanga-zanga
Kotun Tarayya ta yi fatali da karar da aka shigar da masu zanga-zanga. Hoto: Bol News.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: Matakin da kotu da dauka

Alkalin kotun, Peter Lifu ne ya yanke hukuncin bayan kin halartar kotun da suka yi duba da babu wani lauya da ya wakilce su, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan sun shigar da korafi kan masu zanga-zanga saboda take musu hakkinsu na yan kasa yayin da ake fito zanga-zangar.

Masu korafin daga yankunan kasar shida sun bukaci kotun ta tilasta daraktan DSS da hafsan tsaro da babban sifetan yan sanda da kuma Ministan Shari'a dakatar da masu zanga-zangar, cewar Channels TV.

Wadanda ke korafi kan masu zanga-zanga

Daga cikin masu korafin akwai Danladi Goje da Buky Abayomi da Adiza Abbo da Ocholi Aduku da Francis John da Nnamdi Eze.

Ragowar kuma su ne Chibuzor Ifeanyi da Fesco Olatunde da Ishaya Istifanus da sauransu.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: CBN ya fadawa 'yan Najeriya gaskiyar halin da za a shiga

Tinubu ya shirya kawo sauyi bayan zanga-zanga

Kun ji cewa Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Atiku Bagudu, ya ce zanga-zangar yunwa da aka yi ta tilasta masu kara buɗe kunne don jin koken ƴan Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa zanga-zangar ta zaburar da gwamnatin tarayya tare da tuna mata ta riƙa sauraren koke da halin da ƴan ƙasa ke ciki.

Bagudu ya ce duk da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya gano kura-kuran da gwamnatocin baya suka tafka, ba ya son a zargin kowa kan halin matsin da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.