Badakalar $1bn: Masu Yi wa Shugaban EFCC Sojan Gona Sun Shiga Hannu

Badakalar $1bn: Masu Yi wa Shugaban EFCC Sojan Gona Sun Shiga Hannu

  • Jami'an hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana cafke wasu matasa hudu
  • Ana zargin gungun matasan da bayyana kansu a matsayin shugaban EFCC, Ola Olukoyede yayin da su ke shirya zamba
  • Matasan sun nemi tsohon Manajan daraktan hukumar kula da tashoshin jirgin ruwa (NPA) ya ba su kudi ko su kama shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Wasu matasa masu karfin hali sun shiga komar hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) bisa zargin sojan gona.

Ana zargin matasan su hudu da hada kai wajen kokarin damfarar tsohon shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa, Mohammed Bello Koko.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

Hukuma
EFCC ta kama matasa masu yi mata sojan gona Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa matasan sun nemi tsohon shugaban da ya ba su Dala Miliyan 1 ko su sa a kama shi, duk da sunan shugaban EFCC, Ola Olukoyede.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan sun shaidawa Mohammed Bello Koko cewa ana zarginsa da harkalla a lokacin ya na shugaban NPA, kuma EFCC na bincikensa.

Yadda EFCC ta kama sojojin gona

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale ya bayyana cewa sun dauki mataki bayan samun labarin ana kokarin damfarar tsohon manajan daraktan NPA.

Mista Oyewale ya ce da samun rahoton ne su ka aike da jami'ansu, har aka yi wa matasan shigo shigo ba zurfi, sannan aka yi ram da su, PM News ta wallafa.

Hukumar EFCC na binciken matasan

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta na binciken wasu matasa hudu bisa zargin karya da neman cin hanci da sunan shugabanta. Zuwa yanzu, EFCC ta ce ta na binciken mutanen hudu, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar binciken ya kammala.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun nuna bajintarsu, an gano yadda aka kashe fitinannen dan ta'adda

EFCC na shirin kama tsohon gwamna

A baya kun ji cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana cewa za ta kama tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

Hukumar na zargin Yahaya Bello na jam'iyyar APC da zamba da sama da fadi da kudin jama'ar jiharsa har N80bn, inda EFCC ta nemi dauki wajen cafko shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.