Shugaban Kwadago Ya Yi Zafafan Bayanai Bayan Fita daga Wajen 'Yan Sanda
- Shugaban kungiyar kwadagon NLC, Joe Ajaero ya yi jawabi bayan barin ofishin rundunar yan sandan Najeriya a Abuja
- Joe Ajaero ya ce babu gudu babu ja da baya kan ƙoƙarin inganta rayuwar ma'aikata a faɗin Najeriya a kowane lokaci
- Yan sandan Najeriya sun gayyaci shugaban 'yan kwadagon ne kan zargin alaƙa da laifuffukan da suka shafi ta'addanci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero ya yi jawabi bayan ya fita daga wajen yan sanda a birnin tarayya Abuja.
Rundunar yan sanda ta gayyaci Kwamred Joe Ajaero amsa tambayoyi ne bisa zargin alaka da ta'addanci da aka yi masa.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Joe Ajaero ya ce ba gudu ba ja da baya a kan aikin inganta rayuwar ma'ikata a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar alakar shugaban kwadago da ta'addanci
Shugaban yan kwadago, Joe Ajaero ya ce zargin da aka yi masa na alaka da ta'addanci magana ce maras tushe.
Saboda haka ya ce babu wani zargi da za a bijiro da shi domin a toshe muryar kungiyar kwadago a Najeriya.
Gwagwarmayar yan kwadagon Najeriya
Shugaban yan kwadagon ya ce dama aikinsu ya shafi gwagwarmaya da jajircewa domin kawo cigaba kuma sun sha fuskantar barazana.
Vanguard ta wallafa cewa Joe Ajaero ya ce tun a lokacin Janar Sani Abacha aka kulle shi tare da Lauya Femi Falana SAN amma ba su ja da baya ba.
NLC za ta cigaba da gwagwarmaya
Joe Ajaero ya ce za su cigaba da matsin lamba ga gwamnatin tarayya wajen samar da walwalar ma'aikata.
Ya ce a yanzu haka za su matsa lamba har sai sun tabbatar an fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi na N70,000.
N70,000: Za a kara albashi a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe ta fitar da sanarwar shirin fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashin N70,000.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da tabbatar da walwalar ma'aikata a jihar Gombe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng