An Cafke Dattijo da Zargin Kasuwanci da Yan Bindiga a Bidiyo, Ya Fadi Lambar Wayarsu
- Wasu jami'an tsaron Community Watch Corps sun cafke wani dattijo da yake harkar kasuwanci da 'yan bindiga a jihar Katsina
- Dattijon mai suna Malam Lawal Jikan Dada ya bayyana yadda yake siyan kayan sata daga miyagun tare da kai wa kasuwa domin riba
- An yi hira da Jikan Dada ne a cikin wani faifan bidiyo inda ya tabbatar da hakan da kuma kiran lambar wayar wani daga cikinsu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Jami'an tsaro sun kama wani mutum da ake zargin yana siyan kayan sata daga 'yan bindiga da ke garkuwa da mutane a jihar Katsina.
Wanda ake zargin mai suna Malam Lawal Jikan Dada ya tabbatar da cewa yana harkokin kasuwanci da yan bindiga.
Yan bindiga: Jami'an tsaro sun cafke dattijo
Jikan Dada ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Zagazola Makama ya wallafa a manhajar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin faifan bidiyon, an gano yadda ake tatsar bayanai daga wanda ake zargin inda ya tona asirin irin barnar da suke yi.
"Ina da alaka da wadannan barayi ta hanyar siyan dabbobi da duk wani kayan sata ina siya daga gare su da suka hada da Sirajo da Bilya Babba da kuma Manu."
"Sannan ina harkar kasuwanci da rikakken dan bindiga, Kachalla inda ya sayar mani da saniya N125,000, na siyar da ita N132,000."
- Lawal Jikan Dada
Jikan Dada ya fadi alakarsa da yan bindiga
Da aka tambaye shi ko ta ya yake kai musu kudin cinikin da suke yi da miyagun, sai Jikan Dada ya kada baki ya ce:
"Kamar Bilya yaro ya turo na ba shi kudinsa, shi kuma Kachalla ya zo kasuwa wata rana na ba shi kudinsa."
- Jikan Dada
Jikan Dada ya ce tabbas yana jin tsoron mu'amala da su amma ya tabbatar da cewa idan Allah ya yarda ba za su yi masa komai ba.
Har ila yau, Jikan Dada ya bayyana wadanda yake da lambar wayarsu daga cikin yan bindigan da suka hada da Bilya wanda har ya karanto lambar.
Bidiyon yadda aka cafke yaran Bello Turji
Kun ji cewa wasu jami'an tsaro sun kama wasu da ake zargin manyan yaran kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ne yayin wata arangama.
A cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa, an gano yadda jami'an tsaron suka daddaure miyagun wadanda suka addabi yankin Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng