An Shiga Tashin Hankali, Soja Ya Harbe Wani Shugaban 'Yan Sanda har Lahira

An Shiga Tashin Hankali, Soja Ya Harbe Wani Shugaban 'Yan Sanda har Lahira

  • Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Zamfara ta yi Allah wadai da kisan da ta zargi wani sojan Najeriya da yi wa jami'in dan sanda
  • Kakakin yan sanda a jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar ya bayyana cewa an kashe dan sandan ne duk da ya nuna katin shaidar aiki
  • Haka zalika ASP Yazid Abubakar ya yi kira na musamman ga hukumomi kan gaggauta bincike tare da daukar matakin da ya dace

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta fitar da sanarwa kan zargin wani soja da kashe wani dan sanda.

Rahotanni sun nuna cewa dan sandan ya hadu da tsautsayi ne yayin da ya isa wani shingen sojoji.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: CBN ya fadawa 'yan Najeriya gaskiyar halin da za a shiga

Zamfara
Soja ya harbe dan sanda a Zamfara. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin yan sanda a jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar ya bayyana yadda lamarin ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Soja ya kashe dan sanda a Zamfara

Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta yi zargin cewa wani sojan Najeriya ya harbe ɗan sanda mai suna SP Halliru Liman har lahira.

An ruwaito cewa SP Halliru Liman shi ne shugaban yan sanda a caji ofis dake Wasagu a jihar Kebbi.

Yadda soja ya kashe dan sanda

ASP Yazid Abubakar ya bayyana cewa SP Halliru Liman yana tafiya zuwa Birnin Kebbi ne ya hadu da tsautsayi a daidai yankin Danmarke a karamar hukumar Bukkuyum.

Ya ce bayan SP Liman ya isa shingen jami'an tsaro ya nuna katin shaidar aiki amma duk da haka wani soja ya harbe shi a kai wanda ya mutu har lahira nan take.

Kara karanta wannan

Yadda soja ya harbe ɗan tsohon shugaban sojoji, ya sace motarsa a Abuja

Yan sanda sun bukaci a yi bincike

Kakakin yan sanda a jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar ya ce sun yi Allah wadai da kisan kuma suna buƙatar a gaggauta yin bincike.

ASP Yazid Abubakar ya ce suna kara kira kan tabbatar da ɗaukar mataki a kan sojan da ake zargi da aikata laifin da zarar an gama bincike.

Yan sanda sun yi alkawari kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan kasar nan ta jaddada kudirinta na dawo da zaman lafiya yankunan da ke fama da ta'addanci.

Babban Sufeton yan sanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun ne ya bayyana haka, inda ya dauki alkawarin aiki tukuru wajen kawo zaman lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng