Yajin Aiki: Matakan da Aka Ɗauka a Taron Gwamnatin Tinubu da ASUU Sun Bayyana

Yajin Aiki: Matakan da Aka Ɗauka a Taron Gwamnatin Tinubu da ASUU Sun Bayyana

  • Gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar matakan shawo kan kungiyar ASUU bayan ta yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya
  • A taron da suka yi ranar Laraba, gwamnati ta hannun ma'aikatar ilimi ta kafa kwamiti da zai sake nazarin bukatun ASUU
  • Da yake jawabi bayan kammala taron, shugaban ASUU ya ce suna fatan a warware komai kafin zama na gaba a Satumba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ilimi ta tarayya ta kafa wani karamin kwamiti da zai sake duba bukatun kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Wannan na zuwa ne yayin da kowane ɓangare ya amince a ɗage zaman zuwa ranar 6 ga watan Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ɗauki mataki na gaba bayan ganawa a Abuja

Tahir Mamman da shugaban ASUU.
Gwamnati ta kafa kwamitin da zai sake duba bukatun kungiyar ASUU Hoto: Tahir Mamman, ASUU
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ce gwamnatin tarayya da ASUU sun cimma wannan matsaya ne a taron sirri da ya gudana a ma'aikatar ilimi ranar Laraba, 28 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta fara lallaɓa ASUU

Taron wanda ya shafe sa'o'i ya samu halartar shugabannin ASUU da ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman da wasu jami'an ma'aikatar ilimi.

Da yake zantawa da manema labarai a karshen taron, Tahir Mamman ya ce an kafa karamin kwamitin da zai sake duba bukatun kungiyar ASUU.

Ministan ya ƙara da cewa kwamitin zai tabbatar da an yi abin da ya dace tare da warware dukkan inda ke da wata matsala a jerin buƙatun malaman jami'o'i.

Kungiyar ASUU na faran a samu matsaya

A nasa bangaren, shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa su na fatan za a warware dukkan batutuwan kafin taron ranar 6 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Gwamnatin tarayya ta sanya labule da ASUU, an samu bayanai

"Mun gana ne don tattauna dukkan batutuwa da kuma nazari a kansu. Mun bai wa gwamnati tsakanin yau zuwa taro na gaba mu ga abin da za su yi."

ASUU dai na neman gwamnati ta inganta tsarin tafiyar da jami'o'i, kama daga gine-gine, harkokin karatu da kuma kasafin kuɗi mai tsoka, rahoton Channels tv.

Dr. Auwal Abdullahi, wani malamin jami'a a Kano ya shaidawa Legit hausa cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta cika alƙawurran da ta ɗauka.

A cewarsa, galibin jami'o'in gwamnati an barsu a baya kuma ga hakkokin malamai da aka rike da daɗewa.

"Ina ganin lokaci ya yi da ASUU za ta jingine zancen haƙuri, akwai abubuwan da ba zan iya faɗa a midiya ba saboda bani da hurumi, amma ya kamata gwamnati ta cika alƙawari.
"Misali batun IPPIS har yanzun da shi ake biyan malaman jami'a albashi, kuma a baya shugaban ƙasa ya ba da umarnin a cire mu. Sannan ga batun kayan aiki, abubuwan da yawa.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Muhimman dalilai 5 da suka sa ASUU ta yi barazanar rufe jami'o'i a Najeriya

"Muna fatan gwamnati mai ci za ta yi abin da ya dace domin mun shirya tafiya yajin aiki," in ji malamin.

Gwamnati ta gano matar dake yi wa Yarbawa barazana

A wani rahoton kuma gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar NiDCOM ta gano bayanan matar nan da aka ji tana yi wa ƴan Najeriya barazana a kasar Kanada.

A wani faifan bidiyo da ya watsu a X, an ji matar tana cewa za ta fara amfani da abinci da abin sha mai guba wajen kashe yarbawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262