Ma’aikatan Hukumar DSS na Murnar Korar Bichi a Bidiyo? Tsohon Darakta Ya Magantu

Ma’aikatan Hukumar DSS na Murnar Korar Bichi a Bidiyo? Tsohon Darakta Ya Magantu

  • Tsohon daraktan hukumar DSS ya yi martani tare da fatali da bidiyon da ake yadawa cewa wasu na murnar korar Yusuf Bichi
  • Mike Ejofor ya ce an dauki wasu daga cikin faifan bidiyon ne tun a shekarar 2018 inda ya caccaki masu yadawa a kafofin sadarwa
  • Ejiofor ya ce ya kamata sabon shugaban hukumar, Ajayi Adeola ya fito ya yi magana kan sahihancin bidiyon da ake yadawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon daraktan hukumar DSS, Mike Ejiofor ya yi magana kan bidiyon da ake yadawa a kafafen sadarwa.

Ejiofor ya ce bidiyon da ake yadawa cewa ma'ikatan DSS na murnar korar Yusuf Bichi tsohon zance ne wanda aka dauka tun 2018.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

Tsohon daraktan DSS ya yi magana kan bidiyon da ake yadawa kan Bichi
Tsohon daraktan DSS ya magantu kan bidiyon da ake yadawa ana murnar barin Yusuf Bichi shugabancin hukumar. Hoto: @OfficialDSSNG.
Asali: Twitter

Tsohon darakta ya magantu kan bidiyon 'DSS'

Tsohon daraktan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Laraba 28 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ejiofor ya ce ya kamata sabon babban daraktan hukumar, Adeola Ajayi ya fayyacewa al'umma matsayin bidiyon da ake yadawa.

"Wasu daga cikin bidiyon sun dade wanda aka dauka tun 2018, ba sababbin bidiyo ba ne."
"Wasu da ke neman hada husuma da kawo rudani a zukatan al'umma suke yada bidiyon a kafafen sadarwa."

- Mike Ejiofor

Ejiofor ya ce wannan wani shiri ne na masu neman kawo rudani inda ya ce DSS hukuma ce da ke da kwararru wanda ya kamata ta yi martani kan lamarin.

Bidiyon da ake yadawa game da Bichi

Ya ce duk wanda ya wallafa bidiyon a kafafon sadarwa ko da tsoho ne ko sabo ya yi ne domin kawo rudani, inda ya ce yana tunanin daraktan zai yi magana a kai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi martani bayan an fara maganar haɗarin zaben APC a 2027

Shafin @econsintelligenc ya wallafa wasu faifan bidiyo guda biyu a manhajar X wanda ke nuna farin cikin ma'ikatan hukumar bayan barin Bichi mukaminsa.

An zargi Bichi da nakasa Hukumar DSS

Kun ji cewa fitaccen dan jarida da ke zama a Birtaniya, Jaafar Jaafar ya caccaki tsohon shugaban DSS, Yusuf Magaji Bichi.

Jaafar ya zargi Bichi da lalata hukumar wurin daukar ma'aikata tare da zama hukumar tsaro ta 'yan APC zalla a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.