Hukumar NCC Ta Sanya Ranar Karshen Rufe Layukan ’Yan Najeriya, Ta Ba Su Shawara

Hukumar NCC Ta Sanya Ranar Karshen Rufe Layukan ’Yan Najeriya, Ta Ba Su Shawara

  • Hukumar NCC ta sanya 14 ga watan Satumbar 2024 a matsayin ranar karshe kan hada layukan kira da lambar NIN
  • NCC ta shawarci masu amfani layukan kira a Najeriya da su tabbatar sun hada layukan da lambar NIN kafin ranar
  • Legit Hausa samu zantawa da wani da aka rufe masa layinsa a ranar Talata 27 ga watan Agustan 2024 a Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar Sadarwa a Najeriya (NCC) ta sanar a ranar karshe domin ba 'yan kasar damar hada layukansu da lambar NIN.

Hukumar ta sanya 14 ga watan Satumbar 2024 a matsayin ranar karshe inda ta shawarci al'umma su tabbatar sun bi umarnin.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya shirya zaben ciyamomi, ya ayyana Juma'a a matsayin ranar hutu

An sanya wa'adin karshe na rufe layukan kira a Najeriya
Hukumar NCC ta sanya wa'adin karshe domin sake rufe layukan da ba a hada su da NIN ba. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Hukumar NCC ta magantu kan rufe layuka

NCC ta bayyana haka ne a cikin waa sanarwa da ta fitar a yau Laraba 28 ga watan Agustan 2024, TheCable ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta ce fiye da mutane miliyan 153 ne suka yi nasarar hada layukansu da lambar NIN.

Ta ce hakan ya nuna 96% sun samu nasarar hada layukansu idan aka yi la'akari 69.7% a watan Janairun 2024, cewar Tribune.

"Domin tabbatar da bin umarnin hada layuka da lambar NIN, Hukumar NCC ta umarci kowa ya tabbatar ya hada lambar da layinsa zuwa ranar 14 ga watan Satumbar 2024."

- Cewar Sanarwar

Hukumar ta ce hada layukan da lambar NIN zai taimaka wurin tabbatar da kara inganta tsaron Najeriya da dakile matsalolinta inda ta shawarci al'umma su ba su hadin kai wurin samar da hakan.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar adawa ta dakatar da ɗan Majalisar Tarayya mai ci, ta jero dalilanta

Tattaunawar Legit Hausa da wani dattijo

Legit Hausa samu zantawa da wani da aka rufe masa layinsa a ranar Talata 27 ga watan Agustan 2024.

Mansur Muhammad ya ce a ranar Talata da magariba ya duba layinsa ya ga an kulle shi.

Ya ce hakan ya faru duk da hada lambar NIN da layin nasa da ya yi a kwanakin baya.

Daga bisani ya tabbatar da cewa ya gyara layin a ranar Alhamis 29 ga watan Agustan 2024 a ofishin MTN a Gombe.

An rufe layukan 'yan Najeriya da dama

A wani labarin, kun ji cewa daruruwan masu amfani da layin MTN ne da cibiyar sadarwar ta rufe masu layukansu sun yi wa ofishin kamfanin da ke Ibadan.

Kamfanin MTN mafi girma a Najeriya da ke da miliyoyin masu amfani da shi ya rufe layukan mutane da dama a fadin kasar da ya jefa su cikin matsala.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke hodar iblis sama da tan 1000, kudinsa ya wuce N57m

MTN ya yi ikirarin cewa wadanda aka rufe masu layukansu sun gaza hada lambar NIN dinsu da layukan nasu kamar yadda kamfanin ya umurta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.