Jami'an Kwastam Sun Cafke Hodar Iblis Sama da Tan 1000, Kudinsa Ya Wuce N5.7m

Jami'an Kwastam Sun Cafke Hodar Iblis Sama da Tan 1000, Kudinsa Ya Wuce N5.7m

  • Hukumar kwastam ta reshen jihar Kwara ta yi nasarar damke hodar iblis kunshi akalla 1, 153 da aka ƙunso a cikin mota
  • Da ta ke tattaunawa da manema labarai a Ilorin, shugabar hukumar a Kwara, Faith Ojeifo ta ce an ɓoye hodar iblis din a Daf
  • Kwamandar hukumar ta kara da cewa kudin ƙwayar ya kai aƙalla Naira Miliyan 57 idan ya shiga kasuwannin kasar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kwara - Jami'an hukumar kwatsam sun yi nasarar damke wata babbar motar DAF da aka ɓoye kunshi 1, 153 na hodar iblis.

Kwamandar hukumar a jihar, Faith Ojeifo ce ta bayyanawa manema labarai haka a ranar Laraba, inda ta ce kudin kwayar ya haura miliyoyin Naira.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

Kwastam
Hukumar kwastam ta kama hodar iblis a Kwara Hoton: Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa an damke motar ne a yankin Yamboa da ke Bukuro a karamar hukumar Baruten da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an kwastam un sun gano an boye hodar a wani boyayyen sashe a motar DAF mai lamba T-25750-LA, kuma kudin hodar ya kai N57,668,448.

"Direban motar hodar iblis ya gudu," Kwastam

Hukumar kwastam a jihar Kwara ta ce direban babbar motar da aka samu da safarar hodar iblis ya tsere ana tsaka da binciken motar.

Shugabar hukumar, Faith Ojeifo ce ta bayyana haka, inda ta ce gudun da direban ya yi ne ya sa jami'ansu su ka kara matsa bincike har aka gano kunshin hodar.

Kwastam ta mika motar hodar iblis ga gwamnati

Kwastam a jihar Kwara za ta mika motar DAF da aka kama dauke da hodar iblis ga gwamnatin tarayya kamar yadda doka ta yi tanadi.

Kara karanta wannan

Pavel Durov: Waye shugaban manhajar telegram da dalilan cafke shi a Faransa?

Hukumar ta ce motar ka kai aƙalla N21.5m, kuma za a mika ta ga gwamnati ne karkashin sashe na 250 na dokar hukumar kwastam na shekarar 2023.

Hukumar kwastam ta kama mota makare da abinci

A baya kun ji cewa jami'an hukumar kwastam ta kama wata tirela da aka makare da wake da niyyar fitar da shi kasar waje yayin da ake yunwa a Najeriya.

Tirelar na dauke da buhunhunan wake akalla 400, wanda kudinsu ya kai Naira Miliyan 61 wanda aka yi yunkurin ficewa da shi ta iyakar Seme zuwa wajen kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.